fbpx
Friday, August 12
Shadow

Zulum ne kadai Tinubu zai zaba a matsayin abokin takararsa idan har yana so yayi nasara akan Atiku, cewar kungiyar masu hannu da tsaki na jam’iyyar APC

Kungiyar masu hannu da tsaki ta jam’iyyar APC a jihohin arewa guda 19 ta bayyana cewa APC zata fadi zabe idan tayi kuskure wurin zabar abokin takarar Bola Tinubu.

Inda kungiyar tace Atiku Abubakar zai kayar da APC ida har bata tashe tsaye ta nemawa Tinubu abokin takara mai karfi sosai ba, domin Atiku dan arewa ne.

Inda a karshe kungiyar tace kamata yayi APC ta zabarwa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu dan takarar irinsu gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum idan tana so ta kayar da PDP a zabe mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.