fbpx
Saturday, September 23
Shadow

ZUWA GA BUHARI: Yanzu Kam Ka Nuna Mana Kafi Jin Koken ‘Yan Kudu Bisaga ‘Yan Arewa>>Haruna Salihu Chizo

Mawaki kuma me wasan Barkwanci Haruna Salihu Chozo wanda aka fi sani da Chizo Germany ya bayyana rashin jin dadinsa da rushe rundunar SARS da gwamnatin tarayya ta yi.

 

Ya bayyana hakan da farantawa wasu kalilan inda yace amma ‘yan Arewa da dama na ganin amfanin Rundunar ta SARS.

 

Ga dai cikakken Rubutun nasa kamar haka:

Ban taba tunanin kasa irin Najeriya mai fama da ta’addanci ace an wayi gari an soke aiyukan jami’an tsaro na SARS ba, saboda kawai a farantawa wasu ‘yan tsirarun mutane marasa tunani da kishin kasa.

A gaskiya shugaban kasa ka tafka babban kuskure na goyon bayan rushe rundunar SARS, domin wannan runduna ta SARS aiyukan da take gudanarwa na alkairi a cikin kasar nan bata dace da wannan mummunan sakamako ba.

‘Yan Yahoo da sauran ‘yan damfara daga kudu ne kadai ke adawa da wannan runduna ta SARS, domin wannan runduna tana hana su gudanarda aiyukansu na damfara kamar yanda yakamata.

Karanta wannan  Za a fara gwajin riga-kafin cutar HIV a Afirka ta Kudu

Amman duk wanda yake zaune a jahohin Katsina,Zamfara
,Sokoto,Borno, yasan amfani da kokarin wannan runduna ta SARS, domin yadda yake farauto ‘yan fashi da makami banga wata rundunar jami’an tsaro dake yin haka ba.

A gani na ba rushe wannan runduna yakamata ace anyi ba, kamata yayyi ace garambawul ne akawa wannan runduna a maimakon rushe ta.

Don haka yanzu ‘yan Arewa ta fito fili cewa duk rubuce-rubuce da kiraye-kiraye da mu ke yi ga gwamnatin shugaba buhari akan matsalar tsaro a Arewa da ‘yan Kudu ne da tuni an magance misu wannan matsala.

Domin a yanzu ba matsalar tsaro suka nemi a magance misu ba, masu bada tsaro suka nemi a kawo misu karshen su, an kuma biya misu da bukatarsu an rushe rundunar SARS.

Ubangiji Allah ka kawo ma yankin mu na Arewa dauki!!.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *