Zuwa Watan Disamba Matatar Man Fetur Ta Fatakwal Za Ta Dawo Aiki, Inji Gwamnatin Nijeriya
Daga Comr Abba Sani Pantami
Gwamnatin Tarayya ta ce da zarar matatar man fetur din ta fara aiki an kawo karshen shigo da man fetur daga kasashen waje, za a cigaba da aikin tace man a cikin gida Nijeriya, kuma man fetur din zai yi arha.
Karamin Ministan Man Fetur Sanata Heineken Lokpobiri ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar duba cigaban aikin da ake yi a kamfanin sarrafa mai na Fatakwal (PHRC) a yau Juma’a, kamar yadda suka bayyana a shafin kamfanin na Facebook.