fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Zuwan Buhari Kan Mulki Na Daga Cikin Manyan Alkairan Da Suka Taba Faruwa A Nijeriya, Cewar Gwamna Badaru Na Jigawa

Daga Abubakar A Adam babankyauta

Gwamna jihar Jigawa, Muhammad Badaru, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na daga cikin alheran da suka taba faruwa a Nijeriya.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a shirin siyasarmu a yau inda ya bayyana nasarorin da aka samu a mulkin Buhari.

Badaru yace ba a lokacin Buhari aka fara fuskantar matsalar ‘yan bindiga ba, domin sakakin shugabannin da suka gabata ne yasa yan ta,adda sukayi karfin da yake addabar Nijeriya ayanzu.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya kwatanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da abu mafi alheri da ya taba faruwa a Najeriya.

A yayin tattaunawa a shirin siyasarmu a yau wacce gidan talabijin na Channels yayi, gwamnan yace an samu manyan nasarori yayin mulkin shugaba buhari.

Mai gabatar da shirin ya tambaya gwamnan ko ya sakankance da abinda takwaransa na APC yace, sai gwamnan yace: “Na yadda gaskiya, na amince dari bisa dari.

Na san abinda na gada, na san matsalolin da na shiga. A wani lokaci na so tserewa. Amma da babu taimakon shugaban kasa Buhari, ba za mu daga kawunanmu a matsayin gwamnoni ba.

Karanta wannan  Taron dangi aka min>>Sanata Dino Melaye kan faduwa zabe

Idan za ku tuna, yayi belin duka jihohi, ya bamu tallafi ta yadda zamu biya albashin wata 18, ina nufin dukkan gwamnoni. Sannan ya bamu tallafin aiwatar da ayyukan more rayuwa.

Gwamnan ya kara da cewa yadda shugaban kasa buhari ke kokarin shawo kan matsalar makiyaya da manoma abun a jinjina masa ne.

Rikicin makiyaya da manoma ya dade a kasar nan kuma ya tsananta ne a halin yanzu saboda shugabannin da suka shude basu mayar da hankali ba.

Idan muka duba halin da ake ciki yanzu, satar jama’a da garkuwa dasu bai fara zamanin Buhari ba, anda dai a nayi a cikin kasar nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.