Monday, March 16
Shadow

Ƴanbindiga sun kashe aƙalla mutum 20 a Zamfara

Rahotanni na cewa ana ci gaba da samun ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga A jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya bayan sauƙin da aka samu a ƴan watannin nan.

Wasu mahara sun shiga garuruwa da dama na ƙaramar hukumar Maru, inda suka kashe aƙalla mutum 20 tare da yin garkuwa da gommai.

Waɗanda BBC ta zanta da su sun ce ƴan bindigar sun shiga garuruwan ne da motoci inda suka kwashi kayan abinci da sauransu.

Wannan dai na zuwa ne bayan nasarorin da sojojin Najeriya suka samu na hallaka wasu daga cikin shugabannin ƴan bindigar a jihar ta Zamfara.

Karanta Wannan  Ba nasarar Allah da Annabi kasar Congo ta yi akan mu ba, Sihiri suka mana>>Inji Kocin Najeriya, Éric Chelle bayan Kasar Congo lallasa Najeriya da ci 4-3 wanda hakan ya hana Najeriya kaiwa ga buga gasar cin kofin Duniya ta 2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *