Gwamnatin Abba a Kano ta biya kudin hayar gida ga diyar Marigayi Ado Bayero
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya biya wa Zainab Jummai Ado Bayero da mamarta tare da dan'uwanta, kudin haya bayan barazanar korarsu a inda suke haya a Lagos.
Gwamnan Kano ya ceto diyar Ado Bayero bayan an fitar da sanarwar korar su daga gidan haya a Legas….
Ya daidai Rikicin ku'din hayar Gimbiyar Kano da dattijuwar mahaifiyarta a Morning Side Suits a Victoria Island.
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kubtar da diyar marigayi Sarkin Kano Zainab Jummai Ado Bayero da dan uwanta da mahaifiyarta a lokacin da ya sasanta kudin hayar Yarima da Gimbiyar Kano na sa'o'i kadan zuwa wa'adin. na sanarwar fitar da su gidan da su ke a Legas.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya isa Le...
Hukumar kula da Shari'a ta Kano ta hukunta wasu alkalai a jihar saboda aikata ba daidai ba.
Alkalai uku ne dai da maga takarda a babban kotun jihar aka hukunta ciki hadda alkalin da yayi yunkurin satar kudi daga asusun wanda ake tuhuma.
Kakakin hukumar Baba Jibo-Ibrahim ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace wadanda ake zargin sune Magistrate Rabi Abdulkadir, Magistrate Talatu Makama, da Magistrate Tijjani Saleh-Minjibir.
Sanarwar tace an dauki matakin ladabtarwar ne dan tsaftace bangaren shari'a na jihar.
Rundunar ƴansanda a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kori ƴandaba daga fadar sarkin Kano domin daƙile ayyukan dabanci a jihar.
Ƴandaba da mafarauta ne suka kasance suna gadin fadar, wadda Sarki Muhammadu Sanusi II ke zaune a cikin ta yanzu.
Wata majiyar jami’an tsaro ta sanar da PRNigeria cewa matakin ‘yan sandan ya biyo bayan rahotannin sirri da aka samu na kwararowar ƴandaba da ƴantauri wato mafarauta daga ƙananan hukumomi zuwa birnin.
Yanzu haka dai ƴansanda sun karbe iko da fadar ta Gidan Rumfa da ta Nasarawa, inda aka tura jami’ai zuwa wuraren da ke da rauni domin tabbatar da doka da oda.
Yayin da Muhammdu Sanusi II ke ci gaba da zama a Gidan Rumfa, sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na zaune ne a fadar sarkin Kano da ke Nasarawa.
A kwanakin baya ne wata kotu...
Mutanen unguwar Jaen a Kano sun koka da ayyukan 'yan daba inda suka nemi daukin Gwamnati kan lamarin.
Wani Bidiyo da ya watsu a shafukan sada zumunta ya nuna yanda matasan ke cin karensu ba babbaka a unguwar.
https://twitter.com/dan_mutangwale/status/1804270313754046935?t=hlC4-9v2DO8CUoCS1X8VOw&s=19
A shekarun baya dai jihar Kano ta yi fama da ayyukan 'yan daba inda suka lafa amma da alama lamarin zai dawo danye.
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Wani lamari da ya faru a Kano ya baiwa mutane mamaki inda aka ga mutane na satar naman shanu daga wata mota daga samu matsala.
An ga mutane na rige-rigen gudu wasu dauke da kawunan shanu biyu wasu daya.
https://www.youtube.com/watch?v=NkZ3yz1QqQY&pp=ygUJZGF0b2RhdHVr
Wannan na zuwane a yayin da ake zargin shuwagabannin a matsayin wanda ke satar dukiyar mutane suna biyewa daga su sai iyalansu.
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Bayan hukuncin kotu kan rushe sabbin masarautun Kano, lamarin ya jawo cece-kuce a jihar inda mahawara ta yi zafi kuma kowane bangare tsakanin gwamnatin Kano, da Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero ke ikirarin yin nasara, Gwamnatin jihar ta sa a rushe gidan sarki na Nasarawa wanda sarki Aminu ke ciki.
A wasu hotuna da bidiyo da suka watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ga yanda motocin rushe gida suka je fadar ta Nasarawa.
Yayin da yake mayar da martani akan wannan lamari, dan gidan Sarki Muhamm...
KUNCIN RAYUWA: An Kama Baŕawoñ Alĺuñañ Makabarta A Kano.
Jami’an Bigilanti ne suka kama mutumin mai suna Bauhari a maƙabartar Unguwa Uku dake karamar hukumar Tarauni a jihar Kano.
A jiyane dai rahotanni suka bayyana cewa, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin rushe fadar Nasarawa wadda sarki Aminu Ado Bayero ke ciki da nufin gyarata.
Saidai tuni jami'an tsaro sukawa fadar kawanya dan hana aiwatar da wannan umarni.
A jiyandai, Tuni har an kai motocin dake rushe gida fadar ta Nasarawa amma lamarin bai tabbata ba.
Tun a jiyan dai, Wasu masu sharhi akan al'amuran yau da kullun ke ganin cewa, wannan umarni kuskurene saboda ba'a kammala shari' ba.
Daya daga cikin masu irin wannan ra'ayi shine, Salihu Tanko Yakasai wanda yace gwamnan zai saka ai masa dariya saboda wannan umarni da ya bayar:
https://twitter.com/dawisu/status/1803884035124474006?t=sGU-jQHoxSU0qi4uYksphQ&s=19
Wannan hukuncin kotu dai ya kawo rudani a Kano inda kowan...
YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano Ta Umarci 'Yan Sanda Da Su Fitar Da Aminu Ado Bayero Daga Gidan Sarki Na Nassarawa dan rusheshi a gina wani.
Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce za ta fara aikin rushe katangar gidan Sarki na Nasarawa da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ke ciki, tana mai cewa "saboda ya lalace".
Gwamnatin ta kuma umarci kwamishinan 'yansandan jihar da ya fitar da Aminu Ado daga gidan bayan hukuncin kotu a yau Alhamis, wanda ta yi iƙirarin cewa ya ba ta nasara a kan ɓangaren da suka shigar da ƙarar.
Kwamashinan Shari'a na Kano Haruna Isa ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a gidan gwamnati, inda ya jaddada cewa bangon ƙaramin gidan sarkin da ke ƙwaryar birnin Kano ya lalace.
"Mun kammala shirye-shirye domin rushewa da kuma sa...