Wace hanya zanbi in iya turanci
Turanci yarene kamar Hausa, Yarbanci ko Fulatanci, idan mutum yasa kanshi zai iya koyonsa cikin kankanin lokaci.
Hanyar da zaka bi ka koyi turanci cikin sauki shine kamar haka:
Ka kasance tare da abokanka dake son koyon turanci.
Kasancewa tare da abokanka Wanda suke son koyon turanci zai sa Ku rika karfafawa juna gwiwa wajan koyon turancin.
A rika yin turancin koda kuwa ana yin kuskure.
Ka rika kokarin yin magana da turancin koda kuwa kana yin kuskure, hakan zaisa ka samu kwarin gwiwar iyawa sosai.
Ka rika karanta litattafan turancin.
Karanta litattafan turancin da lura da yanda ake hada kalma da jimla na taimakawa wajan iya turancin.
Ka rika kallon fina-finan Turanci.
Kallon fina-finan Turancin zai taimaka maka matuka wajan koyon yanda ake magana da Turancin.
...