Rahotanni sun bayyana cewa, Rahama Sadau ta sa an saki Zaharaddeen Sani daga wajan 'yansanda bayan da Hadiza Gabon tun a farko tasa aka kamashi.
Yanzu haka dai rahotanni sun ce Zaharaddeen Sani na gida.
Tun farko dai Hadiza Gabon ce tace matan da basu shiga fin ba kada su shiga, inda Zaharaddeen ya mata martani me zafi.
Da alama, Hadiza Bata ji dadin martanin Abokin sana'arta ba inda tasa aka kamashi.
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wannan hoton nata inda take tare da abokin aikinta dan kasar India.
Ta saka hoton a shafinta na sada zumunta:
Taurarin Fina-finan Hausa, Rahama Sadau da Ali Jita kenan a wadannan hotunan da bidiyo suke shakatawa a kasar waje.
An ga Jita da Rahama dai suna nishadi tare a cikin mota da kan titi.
Ali Jita ne ya saka bidiyon a shafinsa na sada zumunta.
https://www.tiktok.com/@realalijita/video/7375206383370652933?_t=8mpctjMHVyA&_r=1
Da yawan mata da maza na masana'antar Kannywood sukan je kasashen waje dan shakatawa.
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan yayin da take shakatawa a kasar Turkiyya.
Ta saka hotunan a shafinta na sada zumunta inda masoyanta da yawa suka yaba:
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan yayin da take yawon shakatawa a kasar waje.
Rahama dai ta saka hotunan ne a shafinta na sada zumunta inda aka ganta tana tuka mota, a wasu hotunan kuma aka ganta tana bakin kogi.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan inda take tare da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Rahama ta dora hotonne a shafinta na sada zumunta.