Tuesday, September 17
Shadow

Labaran Atiku Abubakar

Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Labaran Atiku Abubakar, Siyasa
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar adawa ta PDP, a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi alla-wadai da harin da aka kai ƙauyen Ƴargoje da ke jihar Katsina, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Harin da ‘yan bindiga suka kai, ya kuma haɗa da garkuwa da mata da kananan yara marasa galihu, lamarin da ya kara ta’azzara wa al’ummar yankin. Da yake nuna alhininsa game da faruwar lamarin, Atiku ya yi ƙarin haske kan harin kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami’an tsaron da ke amsa kiran gaggawa a kauyukan Gidan Tofa da Dan Nakwabo wanda yayi sanadin mutuwar jami’an ‘yan sanda hudu da wasu ‘yan kungiyar sa ido na jihar Katsina guda biyu. “Wannan babban rashi ne, kuma tunanina yana tare da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu,” in ji shi Atiku ya soki matakan da gwa...