
Dangote, Ya Sake Zama Mutumin Da Ya Fi Kowa Kudi A Afirka, Ya Tara Sama Da Dala Biliyan 11
Dangote, Ya Sake Zama Mutumin Da Ya Fi Kowa Kudi A Afirka, Ya Tara Sama Da Dala Biliyan 11
Daga Comr Abba Sani Pantami
Aliko Dangote ya dawo da kambinsa a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afirka bayan da ya yi rasa matsayin ga hamshakin attajirin Afrika ta Kudu.
Adadin kudin Dangote a yanzu na kara haurawa duk da matsin karyewar darajar Naira a cikin kwanakin nan na baya.
A cewar Forbes, dukiyar dan kasuwan na fannin masana'anta ta haura zuwa dala biliyan 11.2 a yau Lahadi, 27 ga Agusta, 2023.
Wannan yana nuna karuwar 8.73% ko kuma dala miliyan 900 a dukiyar tasa idan aka kwatanta da dala biliyan 10.3 da ya mallaka a farkon watan Agusta.
Karin dukiyar Dangote a yanzu ta cike gibin da ke tsakanisa da babban abokin hamayyarsa, hamshakin attajirin Afrika ta Kudu Johann Ruper...