Tuesday, September 17
Shadow

labaran jihar yobe state

Gwamna Buni Ya Yi Watsi Da ‘Yancin Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi

Gwamna Buni Ya Yi Watsi Da ‘Yancin Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi

labaran jihar yobe state, Siyasa
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi watsi da matakin bai wa kananan hukumomin kasar ‘yancin cin gashin kansu. Buni ya bayyana ra’ayinsa ne jim kadan bayan kada kuri’arsa a zaben kananan hukumomi a mazabar sa da ke Buni Gari. “Lokacin da na hau mulki a shekarar 2019, tunanina shi ne in ba kananan hukumomi cin gashin kai. Sai dai abin takaici shi ne kananan hukumomi shida cikin 17 na jihar Yobe ba sa iya biyan ma’aikata albashi. “Saboda haka, hikimar da ke tattare da wannan asusun hadin gwiwa, wanda ya hada da kokarin kananan hukumomi tare da jihar tare da hadin gwiwa wajen aiwatar da wasu ayyuka, ra’ayi ne da aka samu daga wadannan gazawar,” in ji shi. Gwamnan ya kuma bayyana fatansa game da makomar cin gashin kan kananan hukumomi a Najeriya. "Dimokradiyyarmu tana g...