fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Uncategorized

Allah yawa Sarkin Kuwait Rasuwa

Allah yawa Sarkin Kuwait Rasuwa

Uncategorized
Sarkin Kuwait mai shekara 91, Sheikth Saban al-Ahmed al-Sabah, ya rasu. Ana saran kaninsa da suke uba daya, Yarima Sheikh Nawaf al-Ahmed, ya maye gurbinsa. A watan Yuli, aka kai Sheikh Sabah wani asibitin Amurka sakamakon tiyatar da aka yi masa kan wata cuta da ba a bayyana ko mece ce ba Kuwait din. Tun shekara ta 2006 ya ke mulki a kasar da ke yankin Gulf, kuma ya shafe sama da shekaru 50 ya na sa ido kan harkokinta na ketare.
An daure ma’aikaciyar Bankin First Bank, Oreoluwa Adesakin, Shekaru 98 saboda satar miliyan N49

An daure ma’aikaciyar Bankin First Bank, Oreoluwa Adesakin, Shekaru 98 saboda satar miliyan N49

Uncategorized
An gurfanar da wata ma'aikaciyar bankin First Bank, Oreoluwa Adesakin, a gaban kuliya bisa laifin zamba, sannan Mai Shari'a Muniru Olagunju na Babbar Kotun Jihar Oyo ya ba ta hukuncin daurin shekaru 98 a gidan yari. Amma za ta yi shekaru bakwai a kurkuku. An gano Adesakin da aikata laifin zambar kudi a bankin First Bank har zuwa N49,320,652.32. Ta kuma saci dala 368,203.00 na bankin, wanda ta canza zuwa amfanin ta. Adesakin, kafin banki ya gano ta ya kore ta, ta kasance mai gudanar da aikin ta na Canjin Kudi, wanda aka dorawa alhakin aiwatar da biyan ta hanyar hanyar tura kudi ta Western Union da kuma MoneyGram, Ofishin shiyya na Ibadan na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu'annati, (EFCC) ne ya gurfanar da mai laifin a kan tuhume-tuhume 14, da suka hada da sat...
Insha Allah zamu dauki nauyin karatun ‘ya’yan jami’an tsaron da Boko Haram suka kashe da kuma samar musu abin yi>>Gwamna Zulum yayi Alkawari

Insha Allah zamu dauki nauyin karatun ‘ya’yan jami’an tsaron da Boko Haram suka kashe da kuma samar musu abin yi>>Gwamna Zulum yayi Alkawari

Uncategorized
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa zasu dauki nauyin karatun 'ya'yan jami'an tsaron da Boko Haram suka kashe.   Sannan kuma zasu samarwa iyalansu tallafi dan su dogara da kansu, duk da yake cewa babu abinda za'a iya maye rai dashi. Gwamna ya bayyana hakane, jiya a Hedikwatar 'yansanda inda ya gana da iyalan mamatan da Boko Haram ta kashe a harin da ta kai masa a hanyar zuwa Baga. Yace yana mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan amma yana so yace musu sun mutu a matsayin gwaraza duk da dai ba haka aka so ba.   Gwamnan ya kuma je Asibiti dan ganawa da wanda suka jikkata a harin, A Asibitin an shaida cewa mutane 8 ne da suka jikkata a harin aka kaisu inda an baiwa 5 kulawar data kama aka sallemsu sannan 3 na kwance.
Wata Yarinya ta tsere daga gidansu a Jihar Filato zuwa Jihar Ekiti saboda an ce za’a mata Auren dole

Wata Yarinya ta tsere daga gidansu a Jihar Filato zuwa Jihar Ekiti saboda an ce za’a mata Auren dole

Uncategorized
Wata karamar Yarinya 'yar kasa da shekaru 20 ta gudu daga jihar Filato zuwa Jihar Ekiti wajan Dan Uwanta saboda an ce zaa mata auren dole.   Shugabar kungiyar Lauyoyi mata, Lola Aluko ce ta bayyanawa manema labarai haka inda tace lamarin ya farune ranar 17 ga watan Satumba. Tace an kira dan uwan yarinyar da ta je gurinsa mai suna Adamu inda inda aka dankata a hannunsa da sharadin cewa zai rika kai ta ana dubata.   Shi kuwa mahaifinta a can jihar Filato ya sa an kama wani mutun wanda yace shine ya baiwa yarinya kudin mota ta gudu, saidai dsga baya ya sakeshi amma yace idan diyarsa bata dawo ba zai sake sa a kamashi   Kungiyar kare hakkin bil'adama ta shiga lamarin.
Allah yayiwa Dan Bindigar Sarkin Kano Mai Tafari Rasuwa

Allah yayiwa Dan Bindigar Sarkin Kano Mai Tafari Rasuwa

Uncategorized
Mai Tafari Shahararre ne a jihar Kano ga duk wanda ke bibiyar hawan Sallan da Masarautar Kano ke gudanarwa a duk shekara a yayin bukukuwan Sallah.   Mai Tafari Shine jagoran masu harba bindigar Sarki kuma a kan jiyo shi a duk sa'ilin da Sarki da tawagarsa ta Iso. Yaran Mai Tafari Su kan hau layi suna harba bindiga wanada Al'umma dadama ke Nishadantuwa da jin karar bindigar tasu.   Fatan mu dai Allah Ya jikan sa Da Rahama.
Hotunan Kamin Biki na dan Atiku da Amaryarsa, ‘Yar Nuhu Ribadu da zasu yi Aure

Hotunan Kamin Biki na dan Atiku da Amaryarsa, ‘Yar Nuhu Ribadu da zasu yi Aure

Uncategorized
Dan Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Aliyu Atiku Abubakar da Amaryarsa,  'yar gidan tsohon shugaban EFCC, Fatima Nuhu Ribadu zasu yi aure a ranar 3 ga watan October idan Allah ya kaimu.   Za'a daura aurenne a gidan Nuhu Ribadu dake Abuja da misalin karge 10 na safe, kamar yanda katin gayyatar Auren ya nunar.   Hotunan masoyan na kamin biki sun bayyana.      
Wani Matashi ya rataye kansa a jihar Kano

Wani Matashi ya rataye kansa a jihar Kano

Uncategorized
Lamarin dai ya faru ne a wani kauye da ke garin Dawaki a jihar kano, inda al'umar kauyen su ka wayi gari da ganin gawar matashin a jiki wata Bishiya a cikin daji. Kamar yadda 'yar uwa ga mamacin mai suna Hafsa ta shaidawa Shirin Duniya Tumbin giwa cewa, sun samu labarin mutuwar Dan'uwan nata ne washe gari da safe. Shima wani Shaidar gani da ido wanda ya ce a sakaya sunan sa, ya bayyana Cewa Matashin yana fama da Tabin hankali, kuma ya samu lalurar ne tun bayan rasuwar Mahaifin sa. A cewar sa, An dade ana daukan shi zuwa wajan masu magani domin sama masa lafiya. Daga bisani Munyi kokarin jin tabakin Rundunar 'yan sanda amma lamarin ya ci tura.