Tuesday, June 18
Shadow

Abuja

Kalli Hotunan wata maboyar ‘yan Bin-di-ga da ‘yansanda suka gano

Kalli Hotunan wata maboyar ‘yan Bin-di-ga da ‘yansanda suka gano

Abuja, Tsaro
'Yansanda a Abuja sun bankado wata maboyar 'yan Bindiga dake gidan Dogo a cikin daji Kweti dake kusa da babban birnin tarayya, Abuja. Kakakin 'yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta bayyana hakan ga manema labarai inda tace an bankado maboyar ne bayan samun bayanan sirri. An kama mutane 4 da ake zargi bayan da aka yi musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaron. Dukansu sun amsa cewa su masu garkuwa da mutanene. An kubutar da wasu da suka yi garkuwa dasu inda aka mika su hannun 'yan uwansu.
Hotuna: Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja yayi Hadari

Hotuna: Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja yayi Hadari

Abuja, Duk Labarai, Kaduna
Jirgin kasan dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna yayi hadari a yau, Lahadi. Jirgin yayi hadarin ne a daidai Jere. Jirgin ya tashi ne daga Kaduna zuwa Abuja da misalin karfe 8:05 na safiyar ranar Lahadi. Kuma ya sauka daga kan titinsa a daidai garin Jere. Jami'an tsaron sojoji dana 'yansanda sun je wajan da hadarin ya faru. Hukumar NIBS ta sanar da cewa tana sane da faruwar lamarin kuma ta tura jami'anta zuwa wajan.