Sunday, July 21
Shadow

Amfanin Tafarnuwa

Amfanin tafarnuwa da zuma

Amfanin Tafarnuwa
Tafarnuwa da zuma na da matukar amfani ga lafiyar dan adam,ana iya amfani dasu tare ko daban-daban, duka zasu bayar da sakamakon da ake bukata. Ga amfaninsu kamar haka: Tafarnuwa na da matukar amfani wajan bayar da garkuwa akan ciwon zuciya da shanyewar rabin jiki. Binciken masana da yawa ya tabbatar da hakan inda take taimakawa wajan gudanar da jini yanda ya kamata da kuma magance matsalar da ka iya shafar jinin. Kara kaifin kwakwalwa da Kawar da matsalolin tsufa: Duka zuma da tafarnuwa suna da matukar amfani wajan taimakawa mutane kaucewa cutar mantuwa musamman ga wanda suka fara manyanta. Hakanan tafarnuwa musamman wadda ta dade a ajiye na da wasu sinadarai wanda ke taimakawa kara kaifin kwawalwa sosai da kaucewa cutar mantuwa da sauran matsalolin tsufa. Zuma tana ...

Amfanin man zaitun da tafarnuwa

Amfanin Man Zaitun, Amfanin Tafarnuwa
Tafarnuwa da man Zaitun suna da matukar Amfani sosai musamman ga lafiyar zuciya. Suna taimakwa wajan gudanar jini sosai dan haka shansu a cikin abinci yana taimakawa lafiyar zuciya, kuma yana zama garkuwa ga cutar shanyewar rabin jiki. Ana iya amfani da Man Zaitun da Tafarnuwa wajan gasawa ko dafa Kaza da nama da sauran abubuwanda ake gasawa, ana kuma iya cinsa da taliya, makaroni ko shinkafa. Ana iya yin amfani da Man Zaitun da Tafarnuwa kuma ana iya kara wani abin amfanin kamar ganyayyaki haka. Man Zaitun kuma yana kare mutum daga cutar siga da cutar hawan jini, yana kuma kawar da alamun tsufa a jikin fata.