El-Rufa’i ya maka majalisar dokokin Kaduna a kotu
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya shigar da ƙara a gaban kotu, inda yake ƙalubalantar majalisar dokokin jihar kan zarge-zargen da ta yi masa na almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin mulkinsa.
Gwamnan ya shigar da ƙarar ne a ranar Laraba a wata babbar kotun tarayya da ke birnin Kaduna.
Wata sanarwa da tsohon gwamnan ya fitar ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labaru, Muyiwa Adekeye, ta ce Elrufa'i ya shigar da ƙarar ce domin tabbatar da haƙoƙoƙin da yake da shi na kare kai game da binciken da majalisar dokokin jihar ta ce ta yi a kansa.
Lauyan El-Rufa'i, AU Mustapha ya ce tsohon gwamnan ya ɗauki matakin ne ganin cewa yana da hakkin a saurare shi a duk wani mataki na bincike ko kotu da za a ɗauka kansa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
...