
Kungiyar Barcelona ta daga zaben shugabancin ta izuwa ranar 7 ga watan maris
Kungiyar Barcelona ta gudanar da taro a ofishin ta yau tare da shugaban ta na wucin gadi, Carlos Tusquets da kuma sauran yan takarar ta guda uku dake neman shugabancin kungiyar, Joan Laporta,Victor Font da Toni Frexia akan daga zaben shugabancin izuwa ranar 7 ga watan maris.
Barcelona ta gudanar da taron ne wanda ya dauki tsawon awanni biyu domin tattaunawa da wa'yan nan mutanen kuma gabadayan su sun amince da bukatar kungiyar, saboda dokar cutar sarkewar numfashi ta rikita mata asalin tsarin data yi na gudanar da zaben a ranar 24 ga wannan watan.
Dokar cutar sarkewar numfashin data rikita tsarin zaben asali zata daina aiki ne daga ranar 17 ga watan janairu, amma yanzu an kara tsawon kwanakin izuwa ranar 24, wanda hakan yasa Barca ta yanke shawarar daga zaben ta izuwa ranar 7 g...