Tuesday, September 17
Shadow

Siyasa

Tinubu zai dawo Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila

Tinubu zai dawo Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila

labaran tinubu ayau
A yau,Lahadi ne shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu zai dawo gida Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila. Ranar 29 ga watan Augusta ne shugaban ya bar Abuja zuwa Beijing inda ya dan tsahirta a Dubai, UAE. Ya isa Beijing ranar 1 ga watan Satumba. Ranar 2 ga watan Satumba ne dai shugaban ya fara ziyarar a aikace inda ya gana da shugaban kasar China Xi Jinping sannan aka masa fareti da harbin bindiga na ban girma. A taron, Najeriya da kasar China sun sakawa wasu yarjejeniyoyi guda 5 na ci gaban kasashen biyu hannu kamar yanda kakakin shugaban kasar, Bayo Onanuga ya bayyanar. Hakanan shugaban kasar na China Xi Jinping da matarsa, Peng Liyuan sun shiryawa shugaba Tinubu wata liyafar dare wadda aka nuna al'adun kasar Chinan. Daga nan Shugaba Tinubu ya t...
Ashe Shugaba Tinubu korar me magana da yawunsa Ajuri Ngelale yayi, ji bayani dalla-dalla

Ashe Shugaba Tinubu korar me magana da yawunsa Ajuri Ngelale yayi, ji bayani dalla-dalla

labaran tinubu ayau
Rahotanni na ta kara fitowa kan dalilin ajiye aikin me magana da yawun shugaban kasa,Ajuri Ngelale. A ranar Asabar ne dai Ajuri ya ajiye aikin nasa inda ya bayyana dalilan rashin lafiyar danginsa a matsayin abinda yasa ya ajiye aikin. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa fada ne ko rashin jituwa tsakanin Ajuri da wasu na kusa da shugaban kasar yasa ya ajiye aikin. Hakanan a wani sabon Rahoto na kafar FIJ, suma sun bayyana cewa, rashin jituwa ne tsakanin Ajuri da dayan kakakin shugaban Bayo Onanuga inda kowa kw ganin shine babba a tsakanin su. Majiyar tace an yi yunkurij sasantasu amma Ajuri yaki yadda a yi musu sulhu wanda haka tasa daga baya aka koreshi daga aiki. Saidai bayan da aka koreshi daga aikin,ya yi rokon a taimaka masa yayi ritaya da kansa dan idan akace an...
Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Ta Rasu

Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Ta Rasu

Siyasa
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN. Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff Ta Rasu Allah Ya Yi Wa Mahaifiyar Tsohan Gwamnan Jihar Borno, Hajia Aisa Modu Shariff Rasuwa A Wata Asibiti Dake Abuja, Yau Lahadi Tana Da Shekara 93 A Duniya. Za'a Yi Jana'izarta Gobe Litinin Bayan Kammala Sallar Azahar A Gidan Marigayi Galadima Modu Shariff Dake Kan Hanyar Damboa, Maiduguri Jihar Borno. Allah Ya Jikanta Da Rahama! Daga Jamilu Dabawa
Ba’a taba shugaban kwarai mutumin arziki iin Tinubu ba>>Kashim Shettima

Ba’a taba shugaban kwarai mutumin arziki iin Tinubu ba>>Kashim Shettima

labaran tinubu ayau, Siyasa
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban da ba'a taba yin irinsa ba wajan jajircewa da yiwa Najeriya aiki. Ya bayyana hakane jiya kamar yanda jaridar thisday ta bayyana. Yace shugabanci ba da karfin jiki ake yinsa ba, da kaifin tunani ake yinsa dan haka a daina alakanta lafiyar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shugabancin da yake. Ya kuma yi Allah wadai da wadanda suka rika yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dariya a ranar Dimokradiyya data gabata.
DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin cire kowanne irin haraji akan magunguna da kayan asibiti da ake shigowa da su ƙasar nan

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin cire kowanne irin haraji akan magunguna da kayan asibiti da ake shigowa da su ƙasar nan

labaran tinubu ayau, Siyasa
Cire harajin ya shafi kayan asibiti da suka haɗa da magunguna na ƙwayoyi da na ruwa, sirinji da allurai, sanke na rigakafin cizon sauro, abubuwan gwaji na gaggawa, da sauran kayan amfani a asibiti na yau da kullum. Hakazalika, umarnin na shugaban ƙasa zai ƙara ƙarfafawa masana'antun sarrafa magunguna da kayan asibiti na cikin gida wajen kara inganta su da samar da su a wadace. Wannan zai rage farashin magunguna da kuma wadatar su a lunguna da saƙon kasar nan don amfanin ƴan Najeriya.