Tuesday, June 18
Shadow

Nawa ne farashin dala a yau

Nawane Farashin dala a yau, 31/05/2024, Darajar Naira ta fadi

Nawane Farashin dala a yau, 31/05/2024, Darajar Naira ta fadi

Nawa ne farashin dala a yau
Darajar Naira ta fadi a kasuwar canji ta gwamnati a jiya, Alhamis. Kwanaki 3 kenan a jere darajar Nairar na faduwa a kasuwar Gwamnati. A jiyan, an sayi dalar Amurka akan Naira N1,484.76 wanda hakan ke nuna Naira ta samu faduwar 145.2 idan aka kwatanta da farashin ranar Laraba na Naira N1329.65 akan kowace dala. Saidai a kasuwar 'yan Chanji, Nairar ta dan samu tagomashi na Naira 5, inda aka sayi dalar akan Naira N1,485.
Nawane farashin dala a yau 30/05/2024: Naira ta farfado

Nawane farashin dala a yau 30/05/2024: Naira ta farfado

Nawa ne farashin dala a yau
Farashin Naira a kasuwar 'yan canji ta dan farfado a ranar Laraba, 29/05/2024. An sayi dalar Amurka akan Naira 1,375, idan aka kwatanta da farashin da aka sayi dalar ranar Talata watau Naira 1,500, za'a iya cewa farashin Nairar ya farfado. Saidai kuma a kasuwar Gwamnati, farashin Nairar faduwa yayi inda aka sayi dala akan Naira, 1,339.33. Tashi da faruwar Dala dai na daya daga cikin abubuwan dake ciwa Najeriya tuwo a kwarya.
Nawane farashin Dala a yau, 29/05/2024

Nawane farashin Dala a yau, 29/05/2024

Nawa ne farashin dala a yau
Darajar Naira ta dan fara dawowa inda a jiya, Talata aka sayi dalar Amurka akan Naira 1,173 a farashin Gwamnati. A ranar Litinin dai an sayi dalar akan Naira 1,500 ne a farashin Gwamnatin. Shi kuwa farashin Pound an saye shine akan Naira 1,888, sai kuma Euro da aka siya akan Naira 1,630. An sayi dalar Canada akan Naira 1,112. Sai kuma kudin China, Yuan an sayeshi akan Naira 150.