Tuesday, September 17
Shadow

Aloe Vera

Amfanin aloe vera a gaban mace

Aloe Vera
Aloe Vera na da amfani daban-daban a jikin dan Adam Musamman mata. Daya daga cikin amfanin sa a jikin mace shine yana maganin kaikayin gaba. Macen dake fama da kaikayin gaba, tana iya amfani da man Aloe Vera, ko ruwansa, a samu wanda ba hadi a shafa a farji,da yardar Allah za'a samu sauki. Hakanan me fama da fitar farin ruwa a gabanta,itama tana iya amfani da Aloe Vera dan magance wannan matsala. Akwai wani bincike da aka yi dan gano ko Aloe Vera na maganin fitar farin ruwa a gaban mace? An ware mata 9 aka basu Aloe Vera suka rika amfani dashi kuma dukansu sun bayyana cewa sun samu Sauki. Hakanan a wani bincike da aka yi, An gano cewa idan aka hada Aloe Vera da Gurji(Cucumber) suna sawa gaban mace yayi haske.