Tuesday, September 17
Shadow

Tsafta

Gashin gaba

Tsafta
Gashin Gaba ko kuma ace gashin mara gashine dake fitowa a jikin farjin mace da kuma azzakarin namiji wanda alamace dake nuna cewa mutum ya fara girma kuma ya balaga kuma hukuncin shari'a ya hau kansa. Tsaftace gashin gaba yana da muhimmanci dan yana sakawa mutum ya rika samun nutsuwa sannan kuma yana taimakawa wajan hana warin gaba. Yana da kyau a aske gashin gaba, ko da ba'a aske duka ga, a rika rage masa tsawo daga lokaci zuwa lokaci. Sannan kuma idan an barshi a rika wankeshi akai-akai dan idan ba'a kula dashi za'a ga ya kan rika daukar datti ya canja kala ya koma ruwan kasa, har ya rika wari.

Amfanin toka a hammata

Magunguna, Tsafta
Toka na da amfani sosai wajan gyara hammata da hanata wari. Ana amfani da Toka da Lemun tsami wajan tsaftace hammata dan hanata wari da zufa kuma wannan dabarace da aka yi amfani da ita shekaru aru-aru da suka gabata. Ga yanda ake yi kamar haka: Ana samun lemun tsami. Sannan a samu Toka ta itace ko gawayi. A tace tokar sannan a matse lemun tsamin a cikinta, a kwaba, sannan a shafa a hamatar. A bari yayi kamar minti biyar sannan a wanke. Ana iya yin hakan sau 2 a sati. Saidai idan bai karbi fatar ki ba a dakata amfani dashi, misali idan yana sanya yawan kaikai a hamatar ko yana kawo kuraje. Sai a daina a yi amfami da sauran dabarun tsaftace hamata na kasa: YADDA ZA A TSAFTACE HAMMATA Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan filin namu na kwalliya. A yau ...