Wednesday, October 9
Shadow

Amfanin Man Kadanya

Gyaran nono da man kadanya

Amfanin Man Kadanya, Nono
Wasu bayanai sun nuna cewa man kadanya yana sanya nonon mace ya kara cikowa kuma ya mike sosai ko ya tashi tsayen, haka kuma a wani kaulin yana maida tsohuwa yarinya. Watau yana hana fatar nonon tsufa da wuri. Akwai hanyoyi biyu da wasu bayanai na gargajiya sukace ana amfani dasu wajan gyaran nono da man kadanya. Na farko shine, ana hadashi da man wanke baki watau Makilin a shafa akan nono zuwa wani lokaci a wanke. A bayani na biyu kuma, an samo cewa ana samun man kadanya ko man kade shi kadai a rika shafashi akan nono a hankali kamar ana mai tausa. Saidai duka wadannan bayanai basu da inganci a wajan likitoci, hanyoyi ne na gargajiya na gyaran nono a gida. Abinda ya tabbata shine, idan nononki na kaikayi, zaki iya shafa man kade, yana maganin kaikayin nono da kaikayin k...

Amfanin man kadanya a azzakari

Amfanin Man Kadanya
Man kadanya na da amfani sosai a jikin dan adam kuma maza da mata na iya amfani dashi. Wani shahararren likita a kasar Amurka me suna Dr. Debra Jaliman ya bayyana cewa za'a iya shafa man kadanya a kusan dukkan jiki hadda a saman al'aura ta maza da mata. Idan azzakarinka na kaikayi, zaka iya shafa man kadanya dan ya daina. Hakanan idan Azzakarinka na kumbura shima zaka iya shafa man kadanya dan ya daina. Idan Azzakarinka na bushewa sosai musamman lokacin sanyi, shima zaka iya shafa man kadanya. Saidai masana sun yi gargadin kada a saka man kadanya a cikin azzakari ko a shafashi a yi jima'i dashi.

Amfanin man kadanya a gaban mace ga budurwa

Amfanin Man Kadanya
Man Kadanya na da amfani a gaban mace. Masana ilimin kimiyyar lafiya sunce za'a iya amfani da man kadanya dan magance kaikayin gaba na mata da kuma bushewar gaba. Amma ana shafashine kawai a wajen farji ko gaban mace, masana sun yi gargadin kada a rika shafashi a cikin farjin ko gaban macen dan zai iya kawo matsala. Ga masi amfani dashi a matsayin mai musamman idan gaban mace bashi da ruwa dan jin dadin jima'i, shima masana sun yi gargadi a daina yin hakan. Dalili kuwa ba komai bane ake son ya rika shiga gabanace ba saboda shi gaban mace Allah ya halicceshi yana tsaftace kanshi da kanshi, saidai idan an samu larurar rashin lafiya ko kuma girma ya fara kama mace ta tsufa.
Sirrin man kadanya

Sirrin man kadanya

Amfanin Man Kadanya
DAMINA UWAR ALBARKAWannan KADANYA kenan. Itama tana daga cikin 'ya'yan itatuwan da ake samun wadatuwarsu a lokutan DAMINA. Masana sun tabbatar tana dauke da: Vitamins: A, C, E da kuma K Minerals: potassium, magnesium da kuma iron Tana dauke da Antioxidants Nutritional fibre Fatty acids masu Kara lafiyar jiki A irin wannan yanayi da abincin namu sai a hankali, ya kamata mu dinga amfani da ita kuma mu bawa iyalanmu gwargwadon Hali. Allah Ka wadace mu da lafiya, kwanciyar hankali da wadatuwar arziki a duka kasar nan tamu. Man kadanya na taimakawa wajan hana fata tsufa da wuri. Yana hana kaikayin fata. Yana kare fata daga zafin rana. Idan ana amfani da Man kadanya yau da kullun, Yana taimakawa wajan kara Hasken Fata. Ana iya hada man kadanya da man...