Tuesday, September 17
Shadow

Labaran Falasdinawa

Bidiyo Da Duminsa: Kungiyar Hezzbuollaahh ta wulakanta kasar Israela inda ta lalata abinda take tare makamai dashi sannan ta shiga har inda Israelan ke ajiye danyen manta

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kungiyar Hezzbuollaahh ta kasar Lebanon ta lalata makamin da kasar Israela ke amfani dashi wajen tare hare-haren da ake kai mata ta sama. https://twitter.com/Megatron_ron/status/1803054694354342368?t=FVb1OXcTt8H3cSXfN_NBwQ&s=19 Hezbollah dai a yanzu haka ta kai kan inda kasar Israela ke ajiye man fetur dinta na ko ta kwana. Kuma kai tsaye take bayyana abinda ke faruwa ta bidiyo da jirgi me tuka kansa. Lamarin dai inji masana ba karamin abin kunya bane ga kasar ta Israela.
Kalli Hotuna, Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa an kashshe mata sojoji 8 a Gazza

Kalli Hotuna, Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa an kashshe mata sojoji 8 a Gazza

Duk Labarai, Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa, an kashe mata sojoji 8 a Gazza a ci gaba da yakin da take yi da Israela. Kasat ta bayyana sunayensu kamar haka: Sergeant Ez Yeshaya Grover 20Sergeant Or Blomowitz 20Stanislav Kostarev 21Itay Amar 19Eliyahu Moshe 21Eylon Wiss 49Eytan Koplovich 28Wassim Mahmud 23
Hamas ta soki Blinken kan kalamansa game da batun tsagaita wuta

Hamas ta soki Blinken kan kalamansa game da batun tsagaita wuta

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Hamas ta mayar da martani ga suka daga sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken dangane da jan ƙafa wajen amincewa da ƙudurin tsagaita buɗe wuta, inda ta ce ta yi abin da ya kamata game da tattaunawar zaman lafiya. Hamas ta bayyana cewa ta yi abin da ya kamata dangane da sabuwar shawarar tsagaita buɗe wuta da kuma duk shawarwarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta," inda ta banbanta matsayinta da Isra'ila, wanda ta ce ba ta fito fili ta bayyana amincewa da shirin tsagaita buɗe wuta ba. Blinken ya sha ambata cewa Isra'ila ta amince da shawarar tsagaita wuta, kodayake gwamnatin Isra'ila ba ta tabbatar da hakan a hukumance ba. Da yake magana a Qatar a ranar Laraba, Blinken ya bayyana taƙaicin yadda Hamas ta mayar da martani, yana mai cewa Hamas ta gabatar da sauye-sauye...

Tauraruwar Fina-Finan kasar Amurka, Angelina Jolie ta yi Allah wadai da shuwagabannin kasashen Duniya saboda kyalewa da suka yi anawa Falas-dinawa kisan kiyashi

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Tauraruwar Fina-finan kasar Amurka, Angelina Jolie ta yi Allah wadai da kisan da akewa Falasdinawa. Sannan kuma tace Tana zargin shuwagabannin kasashen Duniya da suka saka Ido suna ganin yanda akewa Falasdinawa kisan kiyashi. Jolie dai dama ta kasance me son tallafawa mutane inda a baya ta yi aiki da majalisar dinkin Duniya wajan bada ayyukan agaji.
Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da sulhu da kasar Israela

Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da sulhu da kasar Israela

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da tayin yin Sulhu da kasar Israela. Shugaban Hezbollah din, Hassan Nasrallah ne ya bayyana haka. Fada na ci gaba da kazancewa tsakanin kasar Israela da Hezbollah. Ko da a jiya sai da Hezbollah tawa kasar Israela ruwan bamabamai masu yawa. Kungiyar dai ta Hezbollah ta bayyana cewa tana goyon bayan samun 'yancin Falasdinawa.

Hamas ta mayar da martani kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Hamas ta miƙa martaninta game da daftarin tsagaita wuta a Zirin Gaza da Amurka ta gabatar. Ƙungiyar ta ce ta yi maraba da daftarin mai matakai uku amma kuma tana buƙatar tabbaci daban-daban. Ciki har da cika alƙawarin dawwamammen zaman lafiya da kuma ficewar dakarun Isra'ila gaba ɗaya daga zirin. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya faɗa tuntuni cewa ba zai dakatar da yaƙin ba har sai sun ga bayan Hamas kwatakwata. Sakataren harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da ke ziyara a yankin ya ce alhakin ɗorewar shirin ya dogara amincewar Hamas. Ƙasashen Qatar da Masar sun bayyana cikin wata sanarwa cewa za a ci gaba da tataunawar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu.

Kwamitin sulhu na MDD ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kwamitin sulhu na MDDr ya yi, wani mataki ne na goyon bayan samar da zaman lafiya. Linda Thomas-Greenfield ta ce ƙasashen duniya sun haɗa kai kan yarjejeniyar da za ta ceci rayuka, da mayar da mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su gida da kuma taimaka wa fararen hula Falasdinawa. A rubuce dai ƙudurin na nuna cewa Isra'ila ta amince da yarjejeniyar wadda shugaba Biden ya sanar a watan jiya. Ita ma Hamas ta yi maraba da ƙuri'ar da Majalisar ta kada, amma har yanzu ba ta mayar da martani a hukumance ba. Wakiliyar BBC ta ce Amurka ta ce za ta ba da tabbacin cewa Isra'ila zata yi biyayya ga yarjejeniyar, muddin Hamas ta amince da ita. A yau Talata ne sakataren harkokin wajen Amur...
An kashe sojojin Isra’ila huɗu a Rafah

An kashe sojojin Isra’ila huɗu a Rafah

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe sojojinta hudu a Rafah da ke kudancin Gaza. A cewar wata sanarwa, sun mutu ne a lokacin da wani gini da aka maƙare da bama-bamai ya ruguje. Biyu daga cikin sojojin ƴan shekara 19 ne, wanda ya girme musu kuma yana da shekara 24. Sanarwar ta ƙara da cewa ƙarin wasu sojoji da dama kuma sun samu munanan raunuka. Kimanin sojojin Isra'ila 300 ne suka mutu tun bayan kaddamar da mamaya a Gaza. Yayin da yaƙin ya yi sanadin rasuwar Falasɗinawa 37,000, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas.

Ministan yaƙin Isra’ila ya sauka daga muƙaminsa

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Ministan yaƙi na Isra'ila, Benny Gantz ya fice daga cikin gwamnatin Netanyahu. Yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai, Mista Gantz ya ce firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu ya ƙi bari a samu abin da ya kira 'tabbatacciyar nasara' kan Hamas. Ministan ya ƙara da cewa dole ne Mista Netanyahu ya sanya ranar da za a gudanar da zaɓukan ƙasar. Tun a ranar Asabar mista Gantz ya yi niyyar gabatar da jawabin nasa, to amma sai ya jinkirta saboda kuɓutar da wasu Isra'ilawa da sojojin ƙasar suka yi a Gaza. Ficewar jam'iyyarsa daga gwamnatin, ba zai kawo ƙarshen gwamnatin ba, to amma zai ƙara matsin lamba kan mista Netanyahu kan sukar da yake sha a ciki da wajen Isra'ila. Dama dai tun cikin watan Mayun da ya gabata, Benny Gantz ya yi barazanar yin murabus daga majalisar yaƙin...

Sarkin Saudiyya gayyaci Falasɗinawa 2000 zuwa aikin Hajji

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Shugaban masallatan Harami, kuma sarkin Saudiyya, Salman bin Abdul Aziz Al Saud ya bayar da umarnin gayyatar ƙarin 'yan uwan Falasɗinawa 1,000 da aka kashe a Gaza a matsayin baƙinsa. Cikin wata sanarwa da shafin X na Haramain ya wallafa, sarkin ya bayar umarnin ƙarin gayyatar 'yan uwan Falasɗinawa ne domin halartar aikin hajjin bana. Dama dai tun da farko sarkin ya gayyaci wasu Falasɗinawan 1,000, inda a yanzu adadin Falasɗinawan da da aka kashe 'yan uwansu da sarkin ya gayyata ya kai 2,000.