Tuesday, June 18
Shadow

Katsina

Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Kaduna, Katsina
Sojojin Najeriya sun sun ce sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30.. Cikin wata sanarwa kwamishin harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun rundunar 'Sector 6 Operation Whirl Punch' suka kai a kan iyakar Kaduna da Katsina Ya ƙara da cewa Manjo Janar MLD Saraso ya jagoranci farmaki kan Yadi da mayaƙansa bayan samun rahotannin sirri da sojojin suka samu daga jihar Katsina. Sanarwar ta ce sojojin sun yi ba-ta-kashi da 'yan bindigar a kusa da dajin Idasu, inda suka kashe ‘yan bindiga aƙalla 36 ciki har da Kacahalla Buharin Yadi. Ƙasurgumin ɗan bindigar ...
Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Katsina, Siyasa, Tsaro
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar adawa ta PDP, a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi alla-wadai da harin da aka kai ƙauyen Ƴargoje da ke jihar Katsina, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Harin da ‘yan bindiga suka kai, ya kuma haɗa da garkuwa da mata da kananan yara marasa galihu, lamarin da ya kara ta’azzara wa al’ummar yankin. Da yake nuna alhininsa game da faruwar lamarin, Atiku ya yi ƙarin haske kan harin kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami’an tsaron da ke amsa kiran gaggawa a kauyukan Gidan Tofa da Dan Nakwabo wanda yayi sanadin mutuwar jami’an ‘yan sanda hudu da wasu ‘yan kungiyar sa ido na jihar Katsina guda biyu. “Wannan babban rashi ne, kuma tunanina yana tare da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu,” in ji shi Atiku ya soki matakan da gwa...
Gwamnonin kudancin Najeriya suna son a kafa ƴansandan jiha

Gwamnonin kudancin Najeriya suna son a kafa ƴansandan jiha

Katsina
Ƙungiyar gwamnonin kudu-maso-yammacin Najeriya sun nemi a kafa rundunonin ƴansanda mallakar jihohi. Sai dai kuma sun yi fatali da fafutukar da wasu ke yi na kafa ƙasar Yarabawa zalla. Wannan na cikin ajanda 11 da suka amince da su bayan taron da suka gudanar a Ikeja babban birnin jihar Legas a ranar Litinin. Gwamnonin sun kuma taɓo batun sabon mafi ƙarancin albashi, inda suka yi nuni da cewa zai zo da tsarin tarayya na gaskiya. Matsalar tsaro malace da daɗe tana ciwa jihohin ƙasar tuwo a kwarya, sai dai wasu na ganin kafa ƴansandan jihohin zai taimaka wajen magance matsalar. A baya dai rundunar ƴansandan ƙasar ta yi watsi da irin wannan buƙata ta kafa ƴnsandan jiha a ƙasar.
Mugunta ko cin Amana? Ji yanda shugaban wani kauye a jihar Katsina ya karbi cin hancin Naira dubu dari bakwai(700,000) ya amince aka kaiwa mutanen kauyensa hari har aka kash-she 30

Mugunta ko cin Amana? Ji yanda shugaban wani kauye a jihar Katsina ya karbi cin hancin Naira dubu dari bakwai(700,000) ya amince aka kaiwa mutanen kauyensa hari har aka kash-she 30

Katsina, Tsaro
Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Umar Dikko Radda ya bayyana yanda wani shugaban kauye ya karbi Naira dubu dari bakwai ya amince aka kai hari akan kauyenshi wanda yayi sanadiyyar kisan mutane 30. Gwamnan yace an samu hakanne a Guga dake Bakori. Ya kara da cewa ba zasu kyale ko wanene aka samu da hannu a harkar 'yan Bindigar ba. Saboda rayuwar mutanen jihar tafi ta mutum daya ko wanene shi.