Wednesday, October 9
Shadow

Nazir Ahmad Sarkin Waka

A karshe dai Sarkin Waka ya bayar da hakuri, Saidai ya fito da sabuwar karin magana

A karshe dai Sarkin Waka ya bayar da hakuri, Saidai ya fito da sabuwar karin magana

Kannywood, Nazir Ahmad Sarkin Waka
Nazir Ahmad Sarkin Waka ya fito da sabuwar karin magana wadda ya jefawa 'yan Cryptocurrency. Nazir a shafinsa na sada zumuntar Instagram yace "Ta nan muka fara wai maroki ya ga dan Mining." Ya kara da cewa, "yace ai duk zuciyar daya ce ma'ana a mace" A karshe dai yace ba zai sake yin magana ba amma idan ya baiwa wani haushi a yi hakuri
Ba zata fashe ba>>Nazir Sarkin Waka ya kara tsokanar ‘Yan Crypto

Ba zata fashe ba>>Nazir Sarkin Waka ya kara tsokanar ‘Yan Crypto

Kannywood, Nazir Ahmad Sarkin Waka
Tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin Waka ya bayyana cewa, Cryptocurrency ba zata fashe ba. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta a yayin da ake ci gaba da yakin cacar baki ta yanar gizo shi da 'yan Crypto. Nazir ya kuma kara da cewa ita tunatarwa tana amfanine amma fa ga mumini kuma shi Munimi ba'a cizonsa sau biyu a rami daya. Yace idan Pi bata fashe ba ta yaya wannan zata fashe?
DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yan Crypto sun sa ankulle Tweeter account din Naziru Sarkin Waka

DA ƊUMI-ƊUMI: ‘Yan Crypto sun sa ankulle Tweeter account din Naziru Sarkin Waka

Kannywood, Nazir Ahmad Sarkin Waka
Hakan ya samo asali ne bayan zagin da yayi wa 'yan mining inda yake cewa " Iya mining ɗinka iya talaucin ka" ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da yake yawo a kafofin sada zumunta. Kalaman da mawakin yayi yayi matuƙar da hankulan yan Crypto wanda yakai ga har sun fara fitowa kafofin sada zumunta suna mayar masa da martani, daga bisa ni kuma suka fara turawa mai kampanin tweeter korafin su, wanda daga karshe korafin su ya samu karbuwa har yakai ga an tsaida a shafin sa na tweeter a halin yanzu. Zuwa yanzu sun koma tura korafin su ga sauran kampanonin sada zumunta inda yake da account dasu kama daga facebook, tiktok Instagram. Shin ya kuke ganin matakin da suka ɗauka ?