Hotunan mata 2 da suka fito takarar shugaban kasa a kasar Iran
Mata biyu ne suka fito takarar shugaban kasa a kasar Iran biyo bayan rasuwar tsohon shugaban kasar, Ebrahim Raisi a hadarin jirgin sama me saukar Angulu.
Mace ta farko itace Zohre Elahian wadda 'yar majalisar tarayyar kasar ce kuma tana da karatu har zuwa digiri na 3 watau(Doctorate) a fannin physics.
Sai kuma mace ta biyu me suna, Hamideh Zarabadi wadda itama 'yar majalisar tarayyar kasar ce kuma tana da digiri na 3 watau( Doctorate) a fannin engineering.
Saidai kasancewar Iran kasar Musulmi ce da take riko da addinin musulunci sosai da kamar wuya su yadda su zabi mace a matsayin shugaban kasa.