fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Kiwon Lafiya

Matan da ba sa cin nama za su iya karyewa a kwankwaso – Bincike

Matan da ba sa cin nama za su iya karyewa a kwankwaso – Bincike

Breaking News, Kiwon Lafiya
Matan da ba sa cin nama za su iya fuskantar yiwuwar karyewa a kwankwaso nan gaba a rayuwa, kamar yadda wani bincike ya nuna. Masu binciken sun rika bin rayuwar mata   26,000 na tsawon shekaru 20 kuma sun gano cewa  kashi daya bisa uku na matan da ke cikin rukuni da ba sa cin nama sai  kayan lambu ko kayan itace za su iya samun karaya ko targade fiye da masu cin nama. Kwararru daga Jami'ar Leeds sun ce wasu daga cikin matan da ba sa cin naman na iya rasa sinadaran inganta lafiyar kashi  da tsokar kashi lamarin da ke haifar da hadarin karaya. Sai dai duk da haka mawallafan rahoton sun ce bai kamata wadanda ba sa cin nama su yi watsi da cin kayan lambu da na itace ba.
Wata sabuwar annoba ta sake barkewa a kasar Chana

Wata sabuwar annoba ta sake barkewa a kasar Chana

Breaking News, Kiwon Lafiya
Bayan cutar sarkewar Numfashi ta Covid-19, wata sabuwar annoba ta sake barkewa a kasar Chana. Sunan wannan sabuwar annobar Langya kuma ta kama mutane da dama a kasar kusan 36 na dauke da cuar amma har yanzu bata kashe kowa a cikinsu ba. Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa daga dabbobi ake samun cutar ta Langya kuma tun a shekarar 2018 ta bullo amma sai makon daya gabata hukumar kiwon lafiya ta Taiwan ta gano annobar. Kuma cutar na sanya ciwon jiki da zazzabi da tari da dai sauran su, yayin da hukumar kiwomn lafiyar ke cigaba da bincike akan cutar domin a magance ta.
Kimanin mutane 857 ne dauke da cutar Lassa kuma tashe mutane 164 a Najeriya, cewar hukumar NCDC

Kimanin mutane 857 ne dauke da cutar Lassa kuma tashe mutane 164 a Najeriya, cewar hukumar NCDC

Kiwon Lafiya
Hukumar dake lura da cututtuka a kasar Najeriya ta NCDC ta bayyana cewa a watanni bakwai na farkon wannan shekarar ta 2022, An samu mutane 857 dauke da cutar zazzabin Lassa kuma annobar ta kashe mutane 164 a fadin Najeriya. Cutar zazzabin Lassa ta samu asali ne daga beraye tun a shekarar 1950 amma ba a waye cutar ba sai a shekarar 1969 bayan taske wasu malaman asibiti guda biyi a garin Lassa. Kuma tun wancan lokaci izuwa yanzu wannan annoba ta dauki rayukan al'umma da dama.
Shugaban kasar Amurka Biden ya sake kamuwa da cutar Covid-19

Shugaban kasar Amurka Biden ya sake kamuwa da cutar Covid-19

Breaking News, Kiwon Lafiya
A ranar asabar likitan gidan White House na shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa Joe Biden ya sake kamuwa da cutar sarkewar numfashi. Shugaban kasar ya kamu da cutar ne bayan daya yi gwaje gwaje guda hudu suna nuna cewa bai kamu ba amma ana biyar sai ya nuna cewa yana dauke da cutar. Saboda haka zai cigaba da killace kansa don kare sauran al'ummar dake tare da shi, kuma yace kwanan nan zai samu sauki ya cigaba da aikinsa yadda ya kamata.
Za a hana shan sigari a garin Manchester

Za a hana shan sigari a garin Manchester

Kiwon Lafiya
Gwamnatin kasar Ingila zata hana shan hana shan sigari a cikin kwaryar garin Manchester. Kuma hakan ya biyo baya ne bayan Manchester ta hada kai da kungiyar kiwon lafiya ta duniya bakidaya don yaki da cutar kansa da dai dai sauran cututtukan da hayake ka iya kawowa. Wuraren da za a hana shan taba a garin sun hada da yankin filin wasan kungiyar Chelsea na Etihad da kuma Piccadilly Gardens, St Peter's Square da dai sauran su.
Da Dumi Duminsa: Hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO ta tabbatar da barkewar cutar Monkeypox a fadin duniya

Da Dumi Duminsa: Hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO ta tabbatar da barkewar cutar Monkeypox a fadin duniya

Breaking News, Kiwon Lafiya
Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta tabbatar da barkewar cutar Monkeypox a fadin duniya. Tedros Ghebreyesus shugaban hukumar ne ya bayyana hakan a yau ranar asabar, biyo bayan barkewar annobar a kasashen duniya. Inda yace akwai wasu kasashen da basu tabbatar da barkewar cutar ba amma duk da haka shi ya tabbatar da ita domin ta fara mamaye duniya. Wannan cutar itace ta farko da hukumar kiwon lafiyar ta tabbatar da barkewarta a fadin duniya bayan Covid-19.
Yanzu Yanzu an samu mutane 74 dauke da cutar Covid-19  jihar Ekiti

Yanzu Yanzu an samu mutane 74 dauke da cutar Covid-19 jihar Ekiti

Kiwon Lafiya
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Ekiti, Oyebanji Filani ya bayyana a yau ranar asabar cewa an samu mutane 74 dauke da cutar Covid-19 a jihar. Likitan yace dole mutane su cigaba da saka takunkumin fuska da kuma wanke hannaye da sabulu ko kuma sinadarin wanke hannu. Inda kuma ya kara da cewa ya kamata mutane su cigaba da zuwa ana yi masu rigakafin cutar domin rage yaduwarta da kuma magance cutar baki daya.
Hukumar NCDC ta yi gargadin cewa sabuwar cutar Marbug Virus data bulla a kasar Ghana ta kuma kashe mutane ka iya shigowa Najariya

Hukumar NCDC ta yi gargadin cewa sabuwar cutar Marbug Virus data bulla a kasar Ghana ta kuma kashe mutane ka iya shigowa Najariya

Kiwon Lafiya
Hukumar kula da harkokin Lafiya ta Najariya, NCDC ta bayyana cewa, cutar Marbug Virus data bulla a kasar Ghana ka iya shigowa Najariya.   Hukumar tace lura da kusancin da Najariya ke da kwai da kasar Ghana ya nuna cewa cikin sauki cutar zata iya shigowa Najariya.   Dan hakane take kira ga mutane da su je a musu gwajin cutar dan kare kawunansu.   Cutar dai ta kama tare da kashe wasu mutane 2 a kasar ta Ghana.   Jami'in hukumar NCDC, Ifedayo Adetifa ya bayyana cewa, suna saka ido sosai kan yiyuwar ballewar wannan cuta a Najeriya.
Cutar Marburg mai yanayi da Ebola ta barke a kasar Ghana, inda har ta dauki rayuka biyu

Cutar Marburg mai yanayi da Ebola ta barke a kasar Ghana, inda har ta dauki rayuka biyu

Kiwon Lafiya
Hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO ta tabbatar da cewa a karin farko an samu mutane biyu dauke da cutar Marburg a yammacin nahiyar Afrika. Inda hukumar ta bayyana cewa mutanen duk yan kasar Ghana ne kuma dukkansu cutar mai kama da Ebola ta kashe su bayan sun kami da ita. Na farkon daya fara kamuwa da cutar dan shekara 26 kuma ya mutu baya kwana guda a asibiti, yayin da shima dai na biyun namijine dan shekara 51 kuma shi a ranar daya je aisbitu ya mutu. A karshe hukumar tace an killace mutane 90 da suka mu'amalanci wa'yanda cutar ta kashe a kasar.