Tuesday, September 17
Shadow

Amfanin Masara

Amfanin tuwon masara

Amfanin Masara
Anan zamu yi magana akan amfanin garin masara da kuma tuwon masara a hade. Garin Masara yana maganin gudawa sosai, hakan yana faruwane saboda fiber ko dusa dake cikinsa. Yana Taimakawa narkewar abinci a cikin mutum. Idan mutum na fama da kashi me tauri ko kuma yana hawa bandaki ya kasa yin kashi, garin masara ko tuwo yana taimakawa sosai. Garin masara ko Tuwo yana taimakawa sosai wajan rage kiba. Garin Masara da tuwo suna maganin ko taimakawa me ciwom zuga. Garin masara ko tuwo yana maganin kumburin jiki. Garin masara ko Tuwo yana maganin yunwa, bayan tuwo, ana iya yin burodi dashi ko a barbada akan abinci irin su dangin cake da sauransu a ci.

Menene amfanin masara ajikin mutum

Amfanin Masara
Masara na da matukar amfani sosai a jikin mutum inda ake amfani da ita wajan yin abubuwan amfani da yawa na yau da kullun. Tana Gyara ido: Masara na da sinadarai irin su carotenoids, da lutein, da zeaxanthin wanda sune ke taimakawa wajan gyaran ido da kara karfinsa. Masara na taimakawa abinci narkewa a cikin jikin mutum musamman saboda fiber dake cikinta. Hakanan tana taimakawa maza sosai wajan karin lafiyar maraina. Masara na taimakawa masu fama da matsalar mantuwa.

Menene amfanin gemun masara

Amfanin Masara
Gemun masara abune da ake samu a danyar masara me launin gwal wanda mafi yawanci yaddashi ake. Amma yana da matukar amfani ga lafiyar dan adam. Wasu daga cikin amfanin gemun masara sun hada da. Maganin hawan jini, yana sanya hawan jini ya sauka sosai saidai masana sun yi gargadin cewa, kada a shashi da yawa ko kuma a rika shanshi tare da maganin hawan jini saboda zai iya sanya jinin ya sauka fiye da yanda ake bukata. Yana kuma maganin ciwon suga, yana sanya suga ya sauka sosai, saidai masana kiwon lafiya sun yi gargadin kada a rika shanshi tare da maganin ciwon suga dan zai iya sanya suga ya sauka fiye da yanda ake bukata. Yana kuma yin anti-age, watau maganin abubuwan dake kawo saurin tsufa a jiki. Ana kuma amfani dashi wajan rage kiba da maganin ciwon kirji. Saidai mat...