Kada wanda ya kara kiran shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da su an banza na T-Pain>>Fadar shugaban kasa ta yi gargadi
Fadar shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ta yi gargadin kada wanda ya kara kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sunan banza na T-Pain.
Sunan T-Pain dai a kafar sada zumunta aka sakawa shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu shi dan nuna wahalar da mutane ke ciki a karkashin Gwamnatinsa wanda sunan wani mawakin kasar Amurka ne.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar na daga cikin wadanda suka rika kiran Tinubu da wannan suna.
Saidai duk da gargadin da fadar shugaban kasar ta yi,da yawa sun ce ba zasu daina fadar wannan suna ba.