
Ji yanda aka yi daurin auren dan ministan kudi ba tare da kowa ya sani ba saboda yace bai son Almubazzaranci musamman saboda halin da ‘yan Najeriya ke ciki
An daura auren dan ministan Kudi Wale Edun, me suna Mr. Tobi Edun a asirce ba tare da kowa ya sani ba.
Daurin auren ya samu halartar manyan mutane ma'aikatan gwamnati na 'yan kasuwa amma ba'a yi Sharholiya ba.
Ministan kudin ne ya bukaci kada a yi almubazzaranci wajan bikin dan nasa.
Inda ake tsammanin ya dauki wannan mataki ne musamman saboda halin matsin da mafi yawan 'yan Najeriya ke ciki, kamar yadda wata majiya a kusa dashi ta gayawa jaridar Vanguard.