
Wata mata ta rabu da mijinta ta auri dan kishiyarta
Wata mata me shekaru 35 ta rabu da mijinta inda ta koma tana soyayya da dan kishiyarta me shekaru 21, kuma ta bayyana cewa ta je likitoci sun tada mata komada dan ta burge sabon masoyin nata.
Marina Balmesheva 'yar kasar Rasha ta bayyana cewa, tuni ma tana dauke da cikin dan kishiyartata.
Ta bayyana cewa a yanzu itace ke daukar nauyin komai kamin sabon masoyin nata ya samu abin yi.