Tuesday, June 18
Shadow

Tsaro

Hoto: An kamasu sun yiwa matar aure da kawayenta fyade

Hoto: An kamasu sun yiwa matar aure da kawayenta fyade

Tsaro
Hukumar 'yansanda sun kama wadannan 'yan fashin a Abagana dake karamar hukumar Njikoka jihar Anambra. Rahoto yace mutanen sanannun masu yiwa mata fyadene. Sun shiga gidan wata mata inda suka sameta ita da kawayenta suka musu fyade sannan suka sa daya daga ciki ta tura musu kudi. Kakakin 'Yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wanda ake zargin sun amsa laifukansu. Sannan za'a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.
‘Yan Sanda Sun Kwato Motar Sata, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Jigawa

‘Yan Sanda Sun Kwato Motar Sata, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Jigawa

Tsaro
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai suna Mahmud Adam mai shekaru 43 da laifin satar mota, tare da gano motar kirar SUV da aka sace a karamar hukumar Gwaram. DSP Shiisu Adam, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jigawa, ya sanar da hakan a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar, 15 ga watan Yuni. A cewar Shiisu, kama barawon ya biyo bayan rahoton sace wata mota kirar Honda CRV mai lamba DKD 10 AG mallakin Wani Abba Yahya daga garin Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu ta jihar Kano. Ya ce motar tana kan hanyar zuwa Maiduguri jihar Borno. Ya bayyana cewa, jami’in ‘yan sanda (DPO) na Gwaram tare da tawagarsa sun tare motar kirar SUV akan hanyar Sara zuwa Darazo. SHiisu ya ce tuni aka mika wanda ake zargi...
Ƴan bindiga sun sace mutane masu yawa ranar sallah a ƙauyen Dudun Doki na ƙaramar hukumar Gwadabawa ta jihar Sokoto

Ƴan bindiga sun sace mutane masu yawa ranar sallah a ƙauyen Dudun Doki na ƙaramar hukumar Gwadabawa ta jihar Sokoto

Sokoto, Tsaro
ANA BIKIN SALLAH YAN BINDIGA SUN TAFKA MUMMUNAN BARNA A SOKOTO. Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Sokoto, inda suka kashe kuma suka sace mutane da dama da sanyin safiyar Lahadi Maharan sun farmaki kauyen Dudun Doki a karamar hukumar Gwadabawa ta jihar, suka kashe mutane sama da goma, kamar yadda aka ruwaito An ruwaito cewa, har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan lamarin ba. Allah ta'ala yakawo mana zaman lafiya alfarmar Al-qur'ani.
Cutar Amai da gudawa ta barke a Najeriya, mutane 65 sun kamu, 30 sun mu-tu

Cutar Amai da gudawa ta barke a Najeriya, mutane 65 sun kamu, 30 sun mu-tu

Tsaro
Daga watan Janairu na shekarar 2024 zuwa 14 ga watan Yuni Mutane 65 ne suka kamu da cutar amai da gudana inda guda 30 suka mutu. An samu cutarne a kananan hukumomi 96 da ke jihohi 30 a fadin Najeriya kamar yanda hukumar kula da cututtuka ta kasa, NCDC ta bayyanar. Hukumar ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ranar Alhamis dan ankarar da mutane kan lamarin inda tace a yi hankali saboda zuwan ruwan sama.
Hoto: Wannan matashin ya yi garkuwa da kansa ya karbi Naira Miliyan 5 daga gurin mahaifinsa

Hoto: Wannan matashin ya yi garkuwa da kansa ya karbi Naira Miliyan 5 daga gurin mahaifinsa

Tsaro
Wannan wani matashine dan kimanin shekaru 20 wanda ya yi garkuwa da kansa. https://www.youtube.com/watch?v=QMoREHNRpDM?si=Z_vLHKGDPEAc2llB Matashin dai ya jada baki da wanine inda aka kamashi aka daure aka kuma rika dukansa. An nemi mahaifinsa ya biya Naira Miliyan 50 wanda daga baya aka ce ya biya Miliyan 5 ta hanyar Bitcoin. Bayan biyan kudin, asirin matashin ya tonu:
Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a wani hari kan bututun mai a Nijar

Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a wani hari kan bututun mai a Nijar

Tsaro
Wasu ƴan bindiga sun kai wa wata tawagar sojoji da ke sintirin aikin sa ido kan bututun man fetur a garin Tibiri da ke yankin Dosso a kudu maso yammacin Nijar harin kwantan ɓauna inda suka kashe sojoji akalla shida. Rahoton wanda aka wallafa a shafukan sada zumunta ya kara da cewa soja ɗaya ya ɓata sannan an lalata motoci biyu a harin. Rahoton bai bayyana ko an samu asarar rai a ɓangaren ƴan bindigar ba, ko kuma bayyana alakarsu da wasu ƙungiyoyi. Ƴan bindiga dai sun kasance suna gudanar da ayyukansu a wasu sassan Nijar da ke kan iyaka da arewa maso yammacin Najeriya. Har yanzu dai rundunar sojin ƙasar ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba. Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, al'amuran tsaron ƙasar Nijar ke ƙara taɓarɓarewa, inda a lokuta da ...
Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin horas da ƴan awaren IPOB a Abia

Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin horas da ƴan awaren IPOB a Abia

Tsaro
Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar dakarun Task Force Tactical Patrol Squad sun kai wani samame a wani sansanin horas da masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) da takwararta ta ESN a unguwar Ihechiowa na ƙaramar hukumar Arochukwu ta jihar Abia. A yayin farmakin, sojojin sun yi nasarar kutsawa tare da tarwatsa sansanin da kuma lalata dukkan na’urorin horas da mayaƙan da kuma kayayyakin da aka samu a wurin. Rundunar sojin ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntarta na X. Cikin wata sanarwa da da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce samamen da sojojinta suka kai wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da ake yi na daƙile ayyukan ta’addanci da ƙungiyoyin IPOB da ESN ke yi, waɗanda ke da alaka da kalubalen tsaro da tashe-tashen hankula da ake fama da su a kan ‘yan ƙas...
Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Kaduna, Katsina
Sojojin Najeriya sun sun ce sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30.. Cikin wata sanarwa kwamishin harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun rundunar 'Sector 6 Operation Whirl Punch' suka kai a kan iyakar Kaduna da Katsina Ya ƙara da cewa Manjo Janar MLD Saraso ya jagoranci farmaki kan Yadi da mayaƙansa bayan samun rahotannin sirri da sojojin suka samu daga jihar Katsina. Sanarwar ta ce sojojin sun yi ba-ta-kashi da 'yan bindigar a kusa da dajin Idasu, inda suka kashe ‘yan bindiga aƙalla 36 ciki har da Kacahalla Buharin Yadi. Ƙasurgumin ɗan bindigar ...