Gyaran nono lokacin yaye
A yayin da jaririnki ya daina shan nono kika yayeshi. Nononki zai iya daukar kusan kwanaki 5 zuwa 10 yana dan kumburi nan da can, hakan ba matsala bane,duk da ba kowace mace ce ke fuskantar wannan matsala ba.
Idan hakan ya faru dake, zaki iya rika yiwa nonon naki tausa sannan zaki iya rika matso ruwan nonon kadan-kadan.
Hakanan ga wanda nonuwan ke zafi bayan kammala shayarwa, ana iya rika dira ruwan sanyi ko a nade kankara a tsumma me kyau a rika dorawa akan nonon.
Yana da kyau kuma a rika shan ruwa ko abinda ya danganci riwa.
Ana iya shan magungunan rage radadin ciwo irin su Ibuprofen.
Sannan maganar gyaran nono ya koma kamar yanda yake kamin ki dauki ciki kuwa, daya daga cikin hanyoyin da ake samun nasarar hakan shine ta hanyar motsa jiki.
An fi son motsa jikin da zai...