Sunday, July 21
Shadow

Laulayin ciki

Kumburin kafa ga mai ciki

Haihuwa, Laulayin ciki
Mai ciki zata yi fama da kumburin kafa, musamman idan cikin ya fara girma. Hakan na faruwane saboda nauyin abinda ke cikinta. Hakan nasa jini ya rage gudana a kafarki, Musamman idan ana yanayim zafi ko kuma kin dade a tsaye. Bayan girman da abinda ke cikinki yake yi, a yayin da kike da ciki, yawan ruwan dake jikinki yana karuwa. Hakan kuma nasa ciwon kafa. Kafa da gwiwoyinki da tafin kafa da yatsu duk zasu iya kumbura. Yayin da cikinki ke kara girma, kumburin shima zai rika karuwa a hankali. Saidai wannan kumburi idan dai ba ya wuce lissafi ba, bashi da cutarwa ga Mahaifiya ko abinda ke cikinta. Alamomin dake nuna kumburin me ciki me cutarwane kuma yana bukatar kukawar likita Idan lokaci guda kumburin ya karu a fuska, hannu da tafin kafa. Idan ciwon kai me ts...

Alamomin cikin wata tara

Duk Labarai, Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 9, abinda ke cikinki na da cikakkiyar halittar Idanu kuma za'a iya cewa ya cika mutum. A wata 9, abinda ke cikinki ya kai tsawon 12 inches ko ace 30 cm Idanun sun yi kwari sosai zasu iya kallon komai. Gashin da ya lullube jikin jaririn kusan za'a iya cewa ya gama zubewa. Hakanan fatar jikin jaririn ta yi kwari. Yayin da cikin ki ya kai wata tara, zai ci gaba da yi miki nauyi. Alamomin daukar ciki, irin su nankarwa, Rashin lafiyar safe, Kasala, kasa rike fitsari, da sauransu zasu ci gaba har zuwa a haihu. Abinda ke cikinki zai iya yowa kasa, wanda hakan zai rage miki wahalar yin kashi da zafin kirji ko zuciya. Saidai cikin wasu matan bai yo kasa har sai nakuda ta tashi.

Alamomin cikin wata takwas

Duk Labarai, Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 8, abinda ke cikinki ya kai tsawon 11 inches. A daidai lokacinne wani gashi me laushi dake lullube da abinda ke cikinki zai fara zubewa. Idan namiji ne, a wannan lokacinne marainansa zasu zazzago kasa. A wannan watanne zaki rika jin gajiya, sannan zaki rika nishi da kyar. Jijiyoyi zasu iya fitowa rado-rado musamman a kafarki. Zaki iya samun nankarwa. Zafin kirji ko zafin zuciya na iya ci gaba, hakanan zaki iya ci gaba da fama da wahala wajan yin kashi. Fitsari zai iya zubowa yayin da kika zo yin atishawa ko kuma kike dariya. Wadannan abubuwanne zaki yi fama dasu yayin da cikinki ya kai watanni 8.

Alamomin cikin wata uku

Laulayin ciki
Idan cikinki ya kai watanni 3 zai zama yana da tsawon 2–3 inches ko kuma a ce 6–7.5 cm. Yatsun hannuwa dana kafa zasu warware. Kasusuwan abin cikinki zasu fara yin karfi. Fata da farata zasu fara fitowa. Alamun jinsin abinda ke cikinki zasu fara bayyana. Koda zata fara samar da fitsari. Alamun sweat glands zasu bayyana. Ido zai zama a kulle. Duka alamun daukar ciki daga wata na 2 zaki ci gaba da ganinsu a wata na 3 kuma zasu ma iya kara tsanani. Zaki ci gaba da fama da rashin lafiya da safe. Nonuwanki zasu ci gaba da girma. Kan nononki zai kara girma ya kuma kara baki. Nauyinki ba zai karu ba sosai a wata na 3. Mafi yawancin barin ciki na farko-farko ana yinshine a wata na 3.

Alamomin cikin wata biyu

Haihuwa, Laulayin ciki
A sati na 5 zuwa 6, abinda ke cikinki zai fara canjawa inda zai shiga matakin Embryo wanda daga wannan mataki ne za'a fara halitta. Zai dunkule a waje daya wanda zai zama kamar zuciya amma bai gama zama zuciyar ba. Idan aka duba a ma'aunin Ultrasound za'a iya jin yana motsi kamar zuciya. Alamun fitowar hannuwa da kafafu zai bayyana. Halittar da Kwakwalwa, jijiyoyi da sauran manyan sassan jiki zasu fita daga ciki zata bayyana. Alamar bindi zata bayyana. Ya yin da cikin ya cika sati 8, watau wata biyu daidai, zuciya zata bayyana Yatsun hannu da na kafa zasu fara bayyana. Ido, kunne, marfin ido ko fatar ido zasu fara bayyana. Da leben sama. A wata na biyu, har yanzu alamomin daukar ciki suna nan tare dake kamar su zafin nono, kasala, yawan fitsari, zafin kirji ko zuci...

Alamomin cikin wata bakwai

Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 7, zaki iya fuskantar matsala saboda nauyin abinda ke cikinki. Gwiwoyi da kafafuwanki zasu iya kumbura. A wannan lokaci ne ya kamata ki samu ilimi kan haihuwa saboda kina kusa da haihuwar. Canji a jikin uwa bayan da ciki ya kai wata bakwai: Zaki iya samun matsalar rashin bacci. Zaki iya samun matsalar zubewar gashi wanda bayan kin haihu zai dawo. Zaki iya ganin karuwar gashi a fuska, gabanki, hamata, kafa da baya Faratan ki zasu rika girma sosai. A yayin da cikinki ya kai watanni 7 da haihuwa, zaki fuskanci fargaba saboda kin kusa haihuwa, zaki rika tunanin nakuda da rainon yaron. Halartar wajan bitar abubuwan da zaki yi nan gaba wajan haihuwa da bayan haihuwa zai taimaka sosai. Canje-Canjen da ake samu a jikin jariri yayin ...