Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce Isra'ila ta kashe mutum aƙalla 100 a wasu hare-hare ta sama da ta kai ƙasar.
Hakan na kunshe ne cikin sabbin alkaluma da ma'aikatar ta fitar, inda ta ce an kuma jikkata mutum sama da 400.
Kasar Yahudawan Israela sun jefawa kasar Lebanon Rokoki 300 a wani sashi na ci gaba da yakin da suke da kungiyar Hezbollah.
Kasar ta Israela dai a cewarta ta gargadi fararen hula dasu tashi daga kusa da gidajen 'yan kungiyar Hezbollah kamin su kai hare-haren.
Kasar tace ta gano 'yan Kungiyar Hezbollah dake shirin kai mata hare-haren Rokoki shine ta dakile su.
Kungiyar Hezzbuollaahh ta kasar Lebanon ta lalata makamin da kasar Israela ke amfani dashi wajen tare hare-haren da ake kai mata ta sama.
https://twitter.com/Megatron_ron/status/1803054694354342368?t=FVb1OXcTt8H3cSXfN_NBwQ&s=19
Hezbollah dai a yanzu haka ta kai kan inda kasar Israela ke ajiye man fetur dinta na ko ta kwana.
Kuma kai tsaye take bayyana abinda ke faruwa ta bidiyo da jirgi me tuka kansa.
Lamarin dai inji masana ba karamin abin kunya bane ga kasar ta Israela.
Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa, an kashe mata sojoji 8 a Gazza a ci gaba da yakin da take yi da Israela.
Kasat ta bayyana sunayensu kamar haka:
Sergeant Ez Yeshaya Grover 20Sergeant Or Blomowitz 20Stanislav Kostarev 21Itay Amar 19Eliyahu Moshe 21Eylon Wiss 49Eytan Koplovich 28Wassim Mahmud 23
Hamas ta mayar da martani ga suka daga sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken dangane da jan ƙafa wajen amincewa da ƙudurin tsagaita buɗe wuta, inda ta ce ta yi abin da ya kamata game da tattaunawar zaman lafiya.
Hamas ta bayyana cewa ta yi abin da ya kamata dangane da sabuwar shawarar tsagaita buɗe wuta da kuma duk shawarwarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta," inda ta banbanta matsayinta da Isra'ila, wanda ta ce ba ta fito fili ta bayyana amincewa da shirin tsagaita buɗe wuta ba.
Blinken ya sha ambata cewa Isra'ila ta amince da shawarar tsagaita wuta, kodayake gwamnatin Isra'ila ba ta tabbatar da hakan a hukumance ba.
Da yake magana a Qatar a ranar Laraba, Blinken ya bayyana taƙaicin yadda Hamas ta mayar da martani, yana mai cewa Hamas ta gabatar da sauye-sauye...
Tauraruwar Fina-finan kasar Amurka, Angelina Jolie ta yi Allah wadai da kisan da akewa Falasdinawa.
Sannan kuma tace Tana zargin shuwagabannin kasashen Duniya da suka saka Ido suna ganin yanda akewa Falasdinawa kisan kiyashi.
Jolie dai dama ta kasance me son tallafawa mutane inda a baya ta yi aiki da majalisar dinkin Duniya wajan bada ayyukan agaji.
Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da tayin yin Sulhu da kasar Israela.
Shugaban Hezbollah din, Hassan Nasrallah ne ya bayyana haka.
Fada na ci gaba da kazancewa tsakanin kasar Israela da Hezbollah.
Ko da a jiya sai da Hezbollah tawa kasar Israela ruwan bamabamai masu yawa.
Kungiyar dai ta Hezbollah ta bayyana cewa tana goyon bayan samun 'yancin Falasdinawa.
Hamas ta miƙa martaninta game da daftarin tsagaita wuta a Zirin Gaza da Amurka ta gabatar.
Ƙungiyar ta ce ta yi maraba da daftarin mai matakai uku amma kuma tana buƙatar tabbaci daban-daban.
Ciki har da cika alƙawarin dawwamammen zaman lafiya da kuma ficewar dakarun Isra'ila gaba ɗaya daga zirin.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya faɗa tuntuni cewa ba zai dakatar da yaƙin ba har sai sun ga bayan Hamas kwatakwata.
Sakataren harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da ke ziyara a yankin ya ce alhakin ɗorewar shirin ya dogara amincewar Hamas.
Ƙasashen Qatar da Masar sun bayyana cikin wata sanarwa cewa za a ci gaba da tataunawar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kwamitin sulhu na MDDr ya yi, wani mataki ne na goyon bayan samar da zaman lafiya.
Linda Thomas-Greenfield ta ce ƙasashen duniya sun haɗa kai kan yarjejeniyar da za ta ceci rayuka, da mayar da mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su gida da kuma taimaka wa fararen hula Falasdinawa.
A rubuce dai ƙudurin na nuna cewa Isra'ila ta amince da yarjejeniyar wadda shugaba Biden ya sanar a watan jiya.
Ita ma Hamas ta yi maraba da ƙuri'ar da Majalisar ta kada, amma har yanzu ba ta mayar da martani a hukumance ba.
Wakiliyar BBC ta ce Amurka ta ce za ta ba da tabbacin cewa Isra'ila zata yi biyayya ga yarjejeniyar, muddin Hamas ta amince da ita.
A yau Talata ne sakataren harkokin wajen Amur...
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe sojojinta hudu a Rafah da ke kudancin Gaza.
A cewar wata sanarwa, sun mutu ne a lokacin da wani gini da aka maƙare da bama-bamai ya ruguje.
Biyu daga cikin sojojin ƴan shekara 19 ne, wanda ya girme musu kuma yana da shekara 24.
Sanarwar ta ƙara da cewa ƙarin wasu sojoji da dama kuma sun samu munanan raunuka.
Kimanin sojojin Isra'ila 300 ne suka mutu tun bayan kaddamar da mamaya a Gaza.
Yayin da yaƙin ya yi sanadin rasuwar Falasɗinawa 37,000, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas.