Sunday, July 21
Shadow

Gwajin Ciki

Ya mace take gane tanada ciki

Gwajin Ciki
Babbar hanyar da mace take gane tana da ciki shine ta hanyar gwaji. Akwai hanyoyin gwaji da yawa amma mafi inganci itace zuwa Asibiti ko kuma amfani da tsinken gwaji wanda ake kira da pt strip test a gida. Ana iya samun tsinken gwaji a kemis da yawa kuma bashi da tsada, saidai dan samun sakamako mafi kyawu a bari sai bayan kwanaki 10 ko 14 a kamin ayi gwajin cikin bayan yin jima'i, wasu masana ma na cewa a bari sai bayan kwanaki 21 kamin a yi gwajin cikin. Inda wasu kuma ke cewa a bari sai bayan an yi batan wata, watau idan lokacin zuwan jinin al'ada yayi amma ba'a ganshi ba. Ana kuma amfani da hanyoyin gargajiya da yawa wajan gwajin ciki kamar amfani da gishiri, suga, da sauransu amma dai yin amfani da tsinken gwaji yafi tabbas ko kuma aje asibiti. Akwai alamun shigar cik...

Cikin wata biyar

Gwajin Ciki, Haihuwa, Nakuda
Duk da yake cewa kowace mace da irin yanda ta ke daukar cikinta amma a wata 5 da daukar ciki, za'a ga girman cikinki ya bayyana. Jikinki zai fara canjawa yana daidaituwa da yanda cikinki ke kara girma. Ga wasu alamu da ke nuna cewa cikinki ya kai wata 5: Kafafunki zasu Kumbura: saboda nauyin da kika kara saboda cikin dake jikinki, kafafunki zasu iya kumbura, kwanciya a daga kafa sama yana taimakawa wajan magance wannan matsala. Ciwon kwankwaso: Saboda yanda cikinki ke fitowa, bayanki zai rika shigewa ciki wanda hakan zai iya kawo miko ciwon kwankwaso. Juwa: A yayin da jaririnki ya ke girma, yawan jinin dake gudana musamman zuwa kanki zai iya raguwa wanda zai sa ki ji juwa. Mura: Zaki iya fuskantar Mura, hancinki ya toshe ko kuma yayi ta yoyo, kai yana ma iya fitar da jin...

Wata nawa ake haihuwa

Gwajin Ciki
Sanin sanda zaki haihu abune me dadi. Ga bayanin masana ilimin kimiyyar lafiya kan lokacin haihuwa. Yayin da mutane mafi yawanci an fi sabawa da kirgen watanni idan aka zo maganar haihuwa, masana ilimin kimiyyar lafiya na amfani da kwanaki da makonnine. A cewar masana kiwon lafiya, cikakken daukar ciki har zuwa a haifeshi, makonni 40 ne, wanda yayi daidai da watanni 10. Nasan da yawa zasu sha mamaki da jin wannan bayani, to bari kuji abinda masana kimiyyar lafiya suka ce. Yawancin mata suna sanin suna da ciki ne bayan basu ga jinin al'adarsu ba, wanda a wannan lokacin kuma mace ta riga ta kai sati 4 da daukar cikin. To a wannan lokacin kuma saura sati 36 mace ta haihu, wanda shine yayi daidai da watanni 9, yanzu kun gane dalilin koh? Sanin ranar da zaki haihu, yawanci li...

Yawan fitsari ga mai ciki

Gwajin Ciki
Yawan fitsari ga mace me ciki ba matsala bane, alamace ta daukar ciki saidai idan yayi yawa, yakan iya zama cuta. Yawan fitsari na faruwa ne ga mace me ciki saboda yanda jikinta yake canjawa saboda shigar ciki da kuma shirin haihuwa. Yawan fitsari na daga cikin alamun farko na daukar ciki. Yawanci yawan fitsari na farawane a mako na 10 zuwa 13 bayan mace ta dauki ciki. Yawanci mata masu ciki kan yi fitsari sau 6 zuwa 10 a rana. Saidai idan ya wuce haka, yana iya zama na ciwo. Kalan fisarin mace me ciki yakan kara duhu, daga ruwan dorawa, watau Yellow zuwa me ruwan dorawa sosai ko kuma Dark Yellow. Idan mace me ciki ta ji fitsari, yana da kyau, kada ta rikeshi, ta je ta yi, saboda rike fitsari yana da illa ga mace me ciki da danta.

Addu’a ga mai ciki: Addu’ar saukin haihuwa

Addu'a, Gwajin Ciki
Wannan addu'a da zamu baku anan manyan malamai sunce sadidan ce, an gwada akan mata dake nakuda kuma an yi nasara: Saidai kamin mu baku wannan addu'a, ga bayani kamar haka: A binciken masana malamai na sunnah sun ce babu wata addu'a da aka ware wadda aka ce mace me ciki zata rika yi. Malamai sunce akwai dai hadisan karya da ake dangantawa da Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) akan addu'a ga mai ciki. Misali Akwai hadisin da aka ce, A lokacin da fatima(A.S) ta zo haihuwa, Ma'aikin Allah Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yasa Umm Salamah da Zaynab bint Jahsh su zo su karanta mata Ayatul Kursiyyu, da kuma al-A‘raaf 7:54, Yoonus 10:3, da kuma falaki da Nasi, Saidai wannan hadisin karyane, domin karin bayani ana iya duba al-Kalim at-Tayyib (p. 161) na Ibn Taymi...

Cin yaji ga mai ciki

Duk Labarai, Gwajin Ciki
Cin abinci me yaji ga mai ciki bashi da matsala sam ko kadan. Kuma ba zai cutar da dan cikinki ba. Saboda yanayin bakin me ciki, zaki so cin abu me yaji dan kwadayi, masana sun ce zaki iya ci ba tare da matsala ba. Mutane da yawa na da tunanin cewa, abinci me yaji yana da hadari ga mai ciki amma hakan ba gaskiya bane. Saidai a sani ko menene aka yishi ya wuce iyaka zai iya bayar da matsala. Hakanan kowace mace da irin jikinta, wata Yaji zai iya zamar mata matsala, wata kuma bata da matsala dashi. Dan haka kinfi kowa sanin kanki. Yaji zai iya sa zafin kirji ko kuma rashin narkewar abinci wanda duka basu da mummunar illa ga me ciki. Jin kwadayin cin abinci me yaji ba matsala bane ga mace me ciki, ga wasu amfanin da abincin me yaji zai yiwa mace me ciki kamar haka: Ci...

Yadda mai ciki zata kwanta

Gwajin Ciki
Masana sun yi amannar cewa, da zaran ciki ya fara girma, an fi son mace ta kwanta a bangaren jikinta na hagu tare da lankwasa gwiwowin kafarta. Wannan tsarin kwanciya a cewarsu shine mafi jin dadi sannan zai taimakawa gudanar jini a jikin uwar da danta. Hakanan a cewar masanan, wannan salon kwanciyar yana hana kumburar kafar me ciki. Masana kiwon lafiya sunce kwanciyar ruf da ciki bata da illa idan ciki be girma ba amma idan ya girma a daina yinta. Masana sun ce kwanciya a gefen dama yana da illa amma kuma me ciki zata iya kwanciya a gefen dama na dan gajeren lokaci. Hakanan masana sun yi gargadin kada a kwanta rigingine, watau akan baya musamman idan ciki yayi nisa. Kwanciya akan baya na hana jini gudana yanda ya kamata a jikin me ciki da kuma dan dake cikinta. Hakan...

Ya ake gane cikin namiji

Gwajin Ciki
A yayin da kika dauki ciki zaki ta samun mutane suna miki magana da bayyana ra'ayoyinsu akan cewa, namiji ne kike dauke dashi ko mace. Akwai dai maganganu na al'ada da camfe-camfe wanda a wannan rubutu zamu muku bayani dalla-dalla yanda lamarin yace a ilimance. A ilimin likitanci, sun ce da zarar maniyyi ya shiga mahaifane ake tantance cewa namiji ne mace zata haifa ko mace. Hakanan sunce kuma kalar ido, kalar gashi, da sauransu duk daga shigar maniyyi da kwan mace mahaifa duka ake tantancesu. Al'aurar abinda ke cikinki zata fara bayyana ne a yayin da kika kai sati 11 da daukar ciki. Saidai duk da haka, ko da gwaji aka yi a wannan lokacin ba za'a iya tantance namiji ne zaki haifa ko mace ba. Maganganun da basu da inganci da ake amfani dasu wajan cewa kin dauki cikin mace ko...

Yadda ake gane cikin tagwaye

Gwajin Ciki
Babbar hanyar da ake gane cikin tagwaye shine ta yin gwaji. Saidai akwai alamomi na al'ada wanda ake amfani dasu wajan gane cikin tagwaye bisa yanda aka saba gani a wajen masu haihuwarsu: Wadannan alamu na cikin gwaye sune kamar haka: Wadannan alamomi da zaku karanta sukan farune a kwanakin farko-farko na daukar ciki. Za'a ji motsin ciki da wuri. Za'a ji motsin ciki a bangarori daban-daban na cikin. Cikin zai yi girma fiye da yanda aka saba gani a sauran cikkunan da ake dauka. Nauyin jikin me cikin zai karu sosai. A wajan gwaji, na'ura zata nuna zuciyoyi biyu na bugawa. Wadannan sune alamomin dake nuna mace na dauke da Tagwaye, saidai kamar yanda muka fada a farko, babbar hanyar gane Tagwaue itace a yi gwaji. Mace zata iya rika jin wadannan alamomi a jikinta ...

Yadda ake gane motsin ciki

Gwajin Ciki
Ana gane motsin ciki ne idan aka ji wani abu kamar filfilo a ciki. Ana kuma iya jin kamar jaririn ya harba kafa. Mace zata iya jin jijjiga. Lokacin da jariri ke fara motsi a ciki: Jariri na fara motsine a sati na 12 da daukar ciki amma ba zaki ji motsin ba. Idan kin taba haihuwa, zaki iya jin motsin jaririn a sati na 16. Amma idan baki taba haihuwa ba, sai wajan sati na 20 kamin kiji motsin jaririn. Saidai kowace mace akwai lokacin da take jin motsin jaririnta ba lallai ya zama lokaci guda ga kowace me ciki ba. Zaki iya sa jaririnki yayi motsi: Masana sunce zaki iya sa jaririnki yayi motsi, idan kina son hakan, kawai zaki kwanta ne ta bangaren hagu ne. Mafi yawanci, mace takan ji motsin jaririnta bayan ta ci abinci.