Sunday, July 21
Shadow

Haihuwa

Maganin rage zafin nakuda

Haihuwa
Radadin nakuda na daya daga cikin manyan abubuwan dake kayar da gaban mata wanda ke sa su rika neman abinda zai kawo musu saukinsa. A wannan rubutu, zamu kawo muku magunguna na gargajiya wanda likitoci suka tabbatar suna aiki wajan rage zafin Nakuda. Shan Zuma Ta tabbata likitoci sun ce mace me ciki dake shan zuma na samun saukin Nakuda sosai ba kadan ba. Hakanan a lokacin nakudar ana iya baiwa mace me ciki zuma ta rika sha, shima yana taimakawa sosai wajen rage radadin Nakudar. Amfani da Zuma da Dabino Hakanan kuma Hada zuma da Dabino a yi blendinsu a sha, shima yana taimakawa rage zafin nakuda da sawa ta a samu nakuda wadda bata da tsawo, watau a haihu da wuri. Wannan sahihin maganin nakuda ne dan an kwada akan mata da yawa wanda aka yi bincike dasu kuma yayi aiki. Amf...

Kumburin kafa ga mai ciki

Haihuwa, Laulayin ciki
Mai ciki zata yi fama da kumburin kafa, musamman idan cikin ya fara girma. Hakan na faruwane saboda nauyin abinda ke cikinta. Hakan nasa jini ya rage gudana a kafarki, Musamman idan ana yanayim zafi ko kuma kin dade a tsaye. Bayan girman da abinda ke cikinki yake yi, a yayin da kike da ciki, yawan ruwan dake jikinki yana karuwa. Hakan kuma nasa ciwon kafa. Kafa da gwiwoyinki da tafin kafa da yatsu duk zasu iya kumbura. Yayin da cikinki ke kara girma, kumburin shima zai rika karuwa a hankali. Saidai wannan kumburi idan dai ba ya wuce lissafi ba, bashi da cutarwa ga Mahaifiya ko abinda ke cikinta. Alamomin dake nuna kumburin me ciki me cutarwane kuma yana bukatar kukawar likita Idan lokaci guda kumburin ya karu a fuska, hannu da tafin kafa. Idan ciwon kai me ts...

Alamomin cikin wata tara

Duk Labarai, Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 9, abinda ke cikinki na da cikakkiyar halittar Idanu kuma za'a iya cewa ya cika mutum. A wata 9, abinda ke cikinki ya kai tsawon 12 inches ko ace 30 cm Idanun sun yi kwari sosai zasu iya kallon komai. Gashin da ya lullube jikin jaririn kusan za'a iya cewa ya gama zubewa. Hakanan fatar jikin jaririn ta yi kwari. Yayin da cikin ki ya kai wata tara, zai ci gaba da yi miki nauyi. Alamomin daukar ciki, irin su nankarwa, Rashin lafiyar safe, Kasala, kasa rike fitsari, da sauransu zasu ci gaba har zuwa a haihu. Abinda ke cikinki zai iya yowa kasa, wanda hakan zai rage miki wahalar yin kashi da zafin kirji ko zuciya. Saidai cikin wasu matan bai yo kasa har sai nakuda ta tashi.

Alamomin cikin wata takwas

Duk Labarai, Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 8, abinda ke cikinki ya kai tsawon 11 inches. A daidai lokacinne wani gashi me laushi dake lullube da abinda ke cikinki zai fara zubewa. Idan namiji ne, a wannan lokacinne marainansa zasu zazzago kasa. A wannan watanne zaki rika jin gajiya, sannan zaki rika nishi da kyar. Jijiyoyi zasu iya fitowa rado-rado musamman a kafarki. Zaki iya samun nankarwa. Zafin kirji ko zafin zuciya na iya ci gaba, hakanan zaki iya ci gaba da fama da wahala wajan yin kashi. Fitsari zai iya zubowa yayin da kika zo yin atishawa ko kuma kike dariya. Wadannan abubuwanne zaki yi fama dasu yayin da cikinki ya kai watanni 8.

Alamomin cikin wata biyu

Haihuwa, Laulayin ciki
A sati na 5 zuwa 6, abinda ke cikinki zai fara canjawa inda zai shiga matakin Embryo wanda daga wannan mataki ne za'a fara halitta. Zai dunkule a waje daya wanda zai zama kamar zuciya amma bai gama zama zuciyar ba. Idan aka duba a ma'aunin Ultrasound za'a iya jin yana motsi kamar zuciya. Alamun fitowar hannuwa da kafafu zai bayyana. Halittar da Kwakwalwa, jijiyoyi da sauran manyan sassan jiki zasu fita daga ciki zata bayyana. Alamar bindi zata bayyana. Ya yin da cikin ya cika sati 8, watau wata biyu daidai, zuciya zata bayyana Yatsun hannu da na kafa zasu fara bayyana. Ido, kunne, marfin ido ko fatar ido zasu fara bayyana. Da leben sama. A wata na biyu, har yanzu alamomin daukar ciki suna nan tare dake kamar su zafin nono, kasala, yawan fitsari, zafin kirji ko zuci...

Alamomin cikin wata bakwai

Haihuwa, Laulayin ciki
A yayin da cikinki ya kai watanni 7, zaki iya fuskantar matsala saboda nauyin abinda ke cikinki. Gwiwoyi da kafafuwanki zasu iya kumbura. A wannan lokaci ne ya kamata ki samu ilimi kan haihuwa saboda kina kusa da haihuwar. Canji a jikin uwa bayan da ciki ya kai wata bakwai: Zaki iya samun matsalar rashin bacci. Zaki iya samun matsalar zubewar gashi wanda bayan kin haihu zai dawo. Zaki iya ganin karuwar gashi a fuska, gabanki, hamata, kafa da baya Faratan ki zasu rika girma sosai. A yayin da cikinki ya kai watanni 7 da haihuwa, zaki fuskanci fargaba saboda kin kusa haihuwa, zaki rika tunanin nakuda da rainon yaron. Halartar wajan bitar abubuwan da zaki yi nan gaba wajan haihuwa da bayan haihuwa zai taimaka sosai. Canje-Canjen da ake samu a jikin jariri yayin ...

Cikin wata hudu

Haihuwa, Lauyayin ciki, Nakuda
Bayan cikinki ya kai wata 4, ga abubuwan dake faruwa: Dan dake cikinki ya kai girman inchi 3 ko ace 8 cm. Za'a iya gane wane jinsi ne abinda ke cikinki saboda za'a iya ganin al'aurarsa a na'urar gwaji ta Ultrasound. Gashin kan abinda ke cikinki ya fara fitowa. An halicci saman baki ko lebe. Da yawa daga cikin Alamomin farko da kika fara ji na daukar ciki zasu daina damunki bayan da cikinki ya kai watanni 4. Saidai matsalolin rashin narkewar abinci zasu iya ci gaba da bayyana a jikinki, kamar wahala wajan yin kashi, zafin kirji ko zuciya. Nononki zai kara girma, zai rika zafi sannan kan nononki zai kara yin baki. Zaki iya samun matsalar numfashi sama-sama ko kuma yinshi da sauri. Dasashin bakinki zai iya yin jini, zaki iya yin habo, watau zubar da jini ta hanci,...

Cikin wata biyar

Gwajin Ciki, Haihuwa, Nakuda
Duk da yake cewa kowace mace da irin yanda ta ke daukar cikinta amma a wata 5 da daukar ciki, za'a ga girman cikinki ya bayyana. Jikinki zai fara canjawa yana daidaituwa da yanda cikinki ke kara girma. Ga wasu alamu da ke nuna cewa cikinki ya kai wata 5: Kafafunki zasu Kumbura: saboda nauyin da kika kara saboda cikin dake jikinki, kafafunki zasu iya kumbura, kwanciya a daga kafa sama yana taimakawa wajan magance wannan matsala. Ciwon kwankwaso: Saboda yanda cikinki ke fitowa, bayanki zai rika shigewa ciki wanda hakan zai iya kawo miko ciwon kwankwaso. Juwa: A yayin da jaririnki ya ke girma, yawan jinin dake gudana musamman zuwa kanki zai iya raguwa wanda zai sa ki ji juwa. Mura: Zaki iya fuskantar Mura, hancinki ya toshe ko kuma yayi ta yoyo, kai yana ma iya fitar da jin...

Ana haihuwa a wata takwas

Haihuwa
Eh, Ana haihuwa a wata takwas amma mafi yawanci dan sai an bashi kulawa ta musamman. Saidai kada ki tayar da hankalinki mafi yawanci duk wanda aka haifa a wata 8 sukan rayu kuma su yi rayuwa irin ta kowa. Kai har wanda ma aka haifa a wata bakwai sukan rayu su kuma yi rayuwa irin ta sauran mutane bayan an basu kulawa ta musamman bayan haihuwarsu. Dan haka idan kika haihu a wata 8 kada hankalinki ya tashi, kiwa abinda kika haifa fatan Alheri. Dalilin da yasa ake haihuwa a wata 8 ko wata 7 wanda ake cewa bakwaini: Idan kofar mahaifarki bata da kwari, ya kai cewa bata iya rike dan da zaki haifa, hakan na iya faruwa, za ta bude ki haihu a wata na 7 ko 8. Idan ya zamana kin taba haihuwa a wata na 7 ko 8, hakan zai iya sake faruwa. Idan 'yan Biyune suma ana iya haihuwarsu lo...

Alamun ciki yakai haihuwa

Haihuwa, Nakuda
Akwai alamu da yada dake nuna ciki ya jai haihuwa: Zaki iya jin zafi sosai kamar na lokacin al'ada. Zaki ji mahaifar ta matse sannan zata saki. Hakan zai iya ci gaba da faruwa, yana zuwa yana tafiya duk bayan mintuna 5, kuma lokaci na tafiya hakan na kara tsananta. Da kinji haka to a kira ungozoma ko kuma a kaiki asibiti, Haihuwa ta zo. Zaki iya jin ciwon baya sosai. A yayin da kike da ciki, wani ruwa me yauki yana taruwa ya kulle kofar mahaifarki, to a yayin da kika zo haihuwa, wannan ruwan zai fito waje, idan kika ganshi, me yauki ne kuma Pink to haihuwa ta zo, saidai wasu na haihuwa ba tare da ganin ruwan ba. Amma masana kiwon lafiya sun ce rashin ganin ruwan ka iya zama alamar cewa akwai matsala tare da ke ko abinda zaki haifa. Dan haka ya kamata a nemi ungozoma k...