
Wata ƙungiyar shugabanni a arewacin Najeriya ta nemi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sauya salon yaƙi da matsalar tsaro bayan harin da Boko Haram ta kai a jihar Borno.
Ƙungiyar Northern Ethnic Nationality Forum ta siffanta lamarin da “bala’i” saboda yadda hare-haren masu iƙirarin jihadi ke hana ayyukan noma da kasuwanci, da kuma garkuwa da mutane da ‘yanbindiga ke yi don neman kuɗin fansa.
A ranar Asabar ne mayaƙan Boko Haram suka kashe sama da mutum 60 bayan harin da suka kai a jihar Borno.
A yau Lahadi ne ƙungiyar ta nemi a naɗa sababbin shugabannin rundunar soja da kuma yi wa majalisar ministoci ta gwamnatin APC garambawul.
Kazalika, sun nemi Shugaba Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a yankin domin yaƙi da matsalar tsaron da ta jawo kashe dubban mutane, musamman a yankin arewa maso yamma.