Ɗaya daga cikin iyayen yaran nan da gwamnatin Najeriya ta tuhuma da cin amanar ƙasa sakamakon zanga-zanga kan tsadar rayuwa ta ce ta yi farin ciki da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya ce a sake su.
Fatima Muhammad ta ce ‘ya’yanta biyu ne cikin yaran da aka kama lokacin da ta aike su karɓo kuɗin za a yi amfani da su wajen kai ɗaya daga cikinsu asibiti saboda ba shi da lafiya.
“Wallahi farin cikin da muka ji ba zai musaltu ba,” in ji Fatima.
Shugabanni da kungiyoyi sun yi tir da kama yaran a wurin zanga-zangar da aka gudanar domin nuna fushi game da tsadar rayuwa daga 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.
Da yake jawabi a fadar shugaban ƙasa, Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce shugaban ƙasa ya ce a sake su duk inda suke a faɗin Najeriya, kuma a sadar da su ga iyayensu.
A ranar Juma’a da ta wuce ne rundunar ‘yansandan Najeriya ta gurfanar da mutum 76 a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda take zargin su da cin amanar ƙasa ta hanyar ɗaga tutar ƙasar Rasha, da kuma neman sojoji su yi juyin mulki, zargin da dukkansu suka musanta.
Shaidu da bidiyon da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna yadda yaran suka rame, jikinsu duk alamun yunwa, kafin daga baya huɗu daga cikinsu su yanke jiki su faɗi lokacin da ake shirin fara yi musu shari’a.
Ɗan Fatima da kuma ɗan ‘yar’uwarta na cikin waɗanda aka kama a birnin Kano, yayin da sauran suka fito daga Katsina, da Gombe, da Abuja, da Jos, da Kaduna.
“An yi tara-tara an kama su ne a Biriget,” in ji Fatima. “Na aike su ne domin karɓo kuɗin wayata [da na sayar] ranar Lahadi saboda zan mayar da shi asibiti.”
Ta ce shekarun ‘ya’yan nata 16 duka biyun saboda sakonnin juna ne.
“Babu inda ban shiga ba ina faman nemansu a ranar nan, amma sai 11:00 na dare aka kira ni aka ce suna [ofishin ‘yansanda na] Bompai. Da na je Allah ya sa na ga maras lafiyar, kuma na ba shi abinci.”
Ta ce lokacin da ta je tana gani ana shirya motocin da za a kai su Abuja.
“Na yi kuka, na yi kuka ina ce musu yarona ba shi da lafiya, amma ‘yansanda suna ce min ‘he is under arrest’, ana korar mu. Su kansu sauran yaran da aka kama suka yi ta ce min mama za mu kula da yaronki. Ina ta kuka, babu wanda ya saurare ni kamar mahaukaciya.”
Daga baya sun yanke shawarar kafa ƙungiya domin fafutikar karɓo ‘ya’yan nasu a matsayinsu na talakawa, kamar yadda Fatima ta bayyana.
‘Kwana a tashoshi da masallatan Abuja’
Hukumomi a Najeriya ba su faɗi ranar da suka kai mutanen da suka kama Abuja ba, amma dai sun tabbatar da cewa duka ana tuhumar su ne a can.
A ranar Juma’ar ne kuma kotun ƙarƙashin Mai Shari’a Obiora Egwuatu ta bayar da belin kowannensu kan naira miliyan 10, da kuma gabatar da mutumin da zai tsaya wa kowa, wanda ta ce dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnati mai matakin albashi na 15.
Lokacin da ta je ofishin ‘yansanda na Bompai a Kano sai aka faɗa mata cewa nan da sati ɗaya za a dawo da su daga Abuja, in ji ta.
“Bayan sati ɗaya ya wuce, aka kira mu a waya aka haɗa mu da su kuma aka ce mu bayar da kuɗin abinci. Da kyar na samo N2,000 na tura musu,” a cewarta.
Bayan haka ne kuma Fatima ta yanke shawarar bin sawun ‘ya’yan nata a Abuja, duk da cewa ba ta san kowa ba a babban birnin tarayyar.
“Lokacin da na tafi [Abuja] ban san kowa ba, ba ni da kowa, ba ni da komai – Allah ne kawai ya tafiyar da al’amurana,” in ji Fatima.
Haka ta yi ta gararamba a tashoshin mota na Abuja, da masallatai.
“Haka na yi faɗi-tashi, na je masallaci na kwana, na je cikin tasha na kwana – wani lokacin sai mutum ya zo sayen abinci sannan ya ce hajiya karɓi na N500.”
‘Sai na biya kuɗi ake bari na ga ‘ya’yana’
Kafin ta je Abuja, Fatima ta ce an kira ta an faɗa mata ɗaya daga cikin ‘ya’yan nata ba shi da lafiya. Bayan ta isa kuma, kullum sai ta je wurin da ake tsare da su.
“Tun da na zo Abuja ban koma gida ba, kullum sai na je wajensu. Wani lokacin ma sai na je na yi bara kafin na samu abin da zan kai musu.
“Lokacin da na fara zuwa, da kyar aka bari na ga ɗaya daga cikin yaran nan kuma sai da na ba da kuɗi. Wani lokacin N1,000 ma ba ta isa, korar mu suke yi har sai ka samu masu kirki ne za su ƙyale ka,” kamar yadda ta yi bayani.
Ta ce tun yaran suna ƙanana aurenta da mahaifinsu ya mutu, kuma yana can kwance yana jinya sakamakon cutar shanyewar ɓarin jiki.
Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce kama yaran ya saɓa wa dokokin ‘yancin ɗan’adam na ƙasa da ƙasa, kuma yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sake “nan take ba tare da wani sharaɗi ba”.
Malam Isa Sanusi, shugaban kungiyar a Najeriya, ya bayyana wa BBC cewar sun kuma nemi a biya diyya saboda “gallazawa da galabaitarwa da yaran suka fuskanta tsawon lokacin da ake tsare a cikin watan Agustan”.
Kwana ɗaya bayan sukar da gwamnatin ta sha, Antoni janar kuma babban lauyan gwamnatin Najeriya, Lateef Fagbemi, ya nemi rundunar ‘yansandan ta miƙa masa lamarin domin cigaba da bibiyar shari’ar.
A ƙarshen mako kuma sai ga Ministar Mata Imaan Sulaiman-Ibrahim ta ziyarci yaran, inda aka gan ta a hotuna tana raba musu ruwa da abinci tare da cin alwashin yi musu adalci.