Friday, May 16
Shadow

Ƴansanda sun ce sun kuɓutar da mutum 10 da aka sace a titin Funtua-Gusau

Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta kuɓutar da mutum goma da ake zargin ƴanbindiga sun yi garkuwa da su a kan babban hanyar Funtua zuwa Gusau.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce an samu nasarar kuɓutar da mutanen ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ƴan bindigar – inda suka kuma daƙile wani yunkurin garkuwa da mutane a kan hanyar ta Funtua-Gusau.

Olumuyiwa ya ce ƴansandan shiyyar Faskari da ke jihar Katsina ne suka yi nasarar kuɓutar da mutanen goma, bayan artabu da masu garkuwan – abin da ya sa suka tsere da munanan raunuka.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna, Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa an kashshe mata sojoji 8 a Gazza

“Jami’an mu sun fafata da ƴanbindigar, abin da ya janyo wasu suka tsere da raunuka. Sakamakon haka muka yi nasarar ceto mutum goma, ciki har da direbobi biyu da kuma fasinjoji takwas. Ba su samu rauni ba kuma mun miƙa su ga iyalansu,” in ji sanarwar ƴansandan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *