Friday, December 5
Shadow

Ƴansanda sun ceto mai shekara 80 daga hannun masu gàrkùwà a Jigawa

Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata tsohuwa mai shekara 80 da aka yi garkuwa da ita daga gidanta da ke ƙaramar hukumar Minjibir a jihar Kano.

Kakakin Rundunar ƴansandan jihar SP Lawan Adam Shiisu Adam ya ce mutanen da suka yi garkuwa da tsohuwar sun ɓoye ta a cikin wani daji na jihar Jigawa mai makwabtaka.

”Bayan sace tsohuwar, barayin sun tafi da ita wasu dazuka da ke tsakanin ƙananan hukumomin Garki da Sule Tankarkar, daga nan ne jami’ansu tare da haɗin gwiwar ƴanbijilanti da na ƙungiyar ƴanbulala suka far wa maharan, bayan ɗauki-b-daɗi kuma suka samu nasarar ceto ta”

Karanta Wannan  Muna da Hujjojin cewa kun aikata laifin cin amanar kasa amma dai Tausayine yasa muka yafe muku>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa kananan yaran da ta yiwa Afuwa

SP Shiisu ya ce jami’ansu sun yi nasarar kama wasu manyan ƴanfashin daji biyar da aka jima ana nema ruwa-a-jallo.

”Daga ciki akwai wanda ma har yana tsallakawa jamhuriyar Nijar ya kuma aikata laifuka a can,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa jami’an sun ƙwato bindigogi irar AK-47 guda biyu, da ƙiarar GPM da aka fi sani da mai jigida, guda ɗaya sai wayoyin hannu da kuma babura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *