
Ƴan majalisar dokokin Najeriya da jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar sun yi watsi da matakin jam’iyyar, tare da bayyana ta a matsayin wadda “ba ta halasta ba”.
A yau Litinin ne shugaban jam’iyyar NNPP a jihar ta Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya sanar da dakatar da ƴan majalisar huɗu daga jam’iyyar bisa zargin su da ayyukan “zagon ƙasa”.
A a tattaunawarsa da BBC, Sanata Kawu Sumaila ya ce “ita kanta wannan jam’iyyar da waɗanda suka yi sanarwar, kotu tana cajin su da cewa su ba halastattun shugabannin jam’iyya ba ne, don haka ba su da iko ko damar ɗaukar wannan mataki.”
A game da batun gayyatar da shugaban jam’iyyar ta NNPP ya bayyana a lokacin sanar da dakatar da ƴan majalisar, Sumaila ya ce “gayyata ce kawai ta zumunci… shi ke nan yanzu jam’iyya sai ta hana ka gayyaci mutane zuwa harkarka?”
A martanin da suka fitar, ƴan majalisar, waɗanda suka haɗa da Sanata Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila, da Kabiru Alhassan Rurum, da Aliyu Sani Madakin Gini da kuma Abdullahi Rogo, sun ce dakatarwar ba wani abu ba ne face “yaudarar siyasa domin kawar da hankalin al’umma daga rashin kataɓus ɗin shugabancin jam’iyyar ɓarin Kwankwaso.”
Sanarwar ta ƙara da cewa jagoran jam’iyyar, Rabi’u Kwankwaso na amfani da “rarrabuwar kawuna a matsayin makami” wajen ci gaba da mallake jam’iyyar.
“Shi ya sa suka ɓuge da bin wannan hanyar ta dakatarwa maras tushe.
“Baya ga cewa wannan mataki haramtacce ne, wani yunƙuri ne kuma daga ɓarin jam’iyyar wanda aka riga aka sallama daga jam’iyyar NNPP, kuma bai ya da hurumi ko kaɗan na ɗaukar irin wannan mataki.”
Ƴan majalisar sun buƙaci al’umma su yi watsi da wannan kora, sannan suka ce suna nan cikin jam’iyyar inda za su yi duk mai yiwuwa “wajen ganin jam’iyyar ta amfani al’umma ba kawai son zuciyar Kwankwaso da muƙarrabansa ba.”