Monday, March 17
Shadow

Ɗansanda ya sha barasa ya saki mutum 13 da ke tsare

Wani jami’in ɗansanda da ya yi mankas da barasa a Zambiya ya saki wasu mutum 13 da ke tsare a ofishin ‘yansanda domin su je su yi shagalin murnar sabuwar shekara.

Jami’ai sun ce an kama sufeto Titus Phiri bayan sakin mutanen da ake tsare da su a wani ofishin ‘yansanda a Lusaka, babban birnin ƙasar.

Mutane 13 da ya saki, ana zarginsu da aikata manyan laifuka da suka haɗa da kisan kai da fashi.

Yanzu haka mutanen sun tsere, kuma tuni aka ƙaddamar da farautarsu.

Karanta Wannan  'Yan ta'adda sun kwace iko da sansanin horas da soji mafi girma a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *