Friday, December 5
Shadow

Ji Yadda aka tsinci Hamdiyya a dajin Zamfara bayan ɓacewarta a Sokoto

Makusantan matashiyar nan da ta yi suna bayan jan hankalin gwamnatin jihar Sokoto kan matsalar tsaro sun tabbatar wa BBC cewa an tsince ta a wani daji na jihar Zamfara bayan batan-dabon da ta yi.

Tun ranar Talata ne aka bayar da rahoton ɓatan Hamdiyya Sidi Sharif, bayan ta fita domin zuwa kasuwa, lamarin da ya sanya ta kasa bayyana a zaman kotu kan shari’ar da ake mata a ranar Laraba a Sokoto.

A watannin baya ne dai gwamnatin jihar Sokoto ta shigar da matashiyar ƙara a gaban kotu, bisa zargin ta da aikata laifin tunzura tayar da zaune tsaye, shari’ar da har yanzu ake gudanar da ita.

A tattaunawarsa da BBC, lauyan da ke kare Hamdiyya, Abba Hikima ya ce yanzu haka tana wani asibiti da ke ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara “cikin mummunan yanayi.”

Ya ce ”wasu mutane ne sanye da kayan ƴansanda suka kama ta a cikin Sokoto, daga nan suka kai ta wani gida a cikin Sokoto, inda suka ɗan azabtar da ita, har ma suka yi mata allura”.

“Bayan yi mata allurar ba ta tashi ganin kanta ba sai a tsakiyar wani daji da ke jihar Zamfara, inda ɓarayi ke kama mutane”, kamar yadda lauyan nata ya shaida wa BBC.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Kalli Bidiyon yanda Mai Wushirya ya yiwa wasu 'yan Tiktok da 'yan Kannywood dake Màdìgò tonon Silili, yace ko sallah basa yi

Ya ƙara da cewa daga dajin ne Allah ya taimaketa ta gudu tare da wani mutum , har suka kai wani ƙauye da ake kira Ƴargeɗa.

Abba Hikima ya ce kawo yanzu matashiyar na samun kulawar likitoci da jami’an tsaro a jihar Zamfara, sai dai ya ce tana cikin mawuyacin hali.

”Ban ganta ba, amma na samu na yi magana da ita (ta waya), kuma bisa ga maganganunta za ka fahimci cewa tana cikin damuwa sosai dukka alamu tana cikin ciwo”, in ji shi.

‘Yadda aka kama Hamdiyya’

Hajiya Zainab Ahmed, da aka fi sani da Bintu Hijazi daya daga cikin makusantan matashiyar ta shaida wa BBC yadda aka kama Hamdiyya.

”Bayan ta kammala cefane ta shiga keke Napep domin komawa gida, sai wani mutum ya tare Napep din sannan ta shiga cikin, bayan sun yi ƴar tafiya, sai wasu mutane sanye da kayan ƴansanda suka tare Napep ɗin, suka zargi mutumin da ya shiga daga baya da shaye-shaye”, in ji ta.

Karanta Wannan  NNPCL ya fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna

”Nan take sai mutumin ya ce ni bana shaye-shaye in ma kun musa ku tambayeta, sai ya juya kan Hamdiyya, sai ita kuma ta ce masa to ni na sanka ne? sai ya ce e mana ba tare muke ba?”.

”Sai ta ce kai mai mashin ka faɗi gaskiya ba daga baya muka ɗauko shi, sai mai mashin ya yi shiru, nan take aka kama su”.

Bintu Hijazi ta ce daga nan aka tafi da su wani gida, inda aka yi mata allura, sannan aka nausa daji da su daji, kafin daga baya su kuɓuta.

Ta ƙara da cewa babau alamar cin zarafi ko raunuka a jikin matashiyar, sai dai rigarta ta ɗan yage sai kuma wuin da aka yi mata allurar.

Bintu Hijazi Ta ce ya zuwa jami’an tsaro ba su yi musu wani bayani kan abin da ya faru da matashiyar ba, amma suna sa ran samun bayanai da zarar an miƙa ta hannun kwamishinan ƴansanda jihar Zamfara.

‘Sau biyu ana sace Hamdiyya’

Wannan ne dai karo na biyu da irin haka ke kasancewa da matashiyar, inda a baya aka taɓa kamata tare da azabar da ita, kamar yadda lauyan nata ya bayyana.

Karanta Wannan  HOTUNA: A karon farko, Sarki Sanusi ya yi hawan Fanisau ba a doki ba

”Kimanin wata shida zuwa bakwai da suka gabata an kama Hamadiyya, inda aka wulaƙanta ta, ta kai har ga an gurɗe mata kafaɗarta, aka kuma jefar da ita cikin daji”, in ji shi.

A farkon watan Nuwamban bara ne matashiyar ta fitar da wani bidiyo a shafukanta na sada zumunta, inda take kokawa game da yadda ‘yanbindiga ke shiga ƙauyensu suna sacewa tare da kashe mutane.

Inda a ciki ta zargi gwamnatin jihar Sokoto da sakaci wajen yaƙi da matsalar tsaro da jihar ke fama da ita.

A martaninta kan zargin gwamnatin jihar ta zargi Hamdiyya da yin kalamai na tunzura jama’a a da haifar da hargitsi a jihar.

Tun bayan bayyanar labarin ɓacewar matashiyar dai ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun ƴan gwagwarmaya ke ci gaba da kiraye-kiraye ga hukumomi su tabbatar da ceto ta.

Ƙungiyar Kare Haƙƙin bila’ada ma Amnesty International ta yi Allah wadai da sace matashiyar, tana mai cewa matashiyar ba ta cancanci hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *