Monday, May 5
Shadow

2027: Baba-Ahmed Ya Bukaci Tinubu Ya Janye, Ya Bar Matasa Su Yi Takara 

2027: Baba-Ahmed Ya Bukaci Tinubu Ya Janye, Ya Bar Matasa Su Yi Takara.

Tsohon mashawarcin shugaban kasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya hakura da shirin neman tazarce, ya bai wa matasa dama su yi takara domin ciyar da kasa gaba a babban zabe na 2027.

A wata budaddiyar wasika da ya aike wa Daily Trust a ranar Laraba, Baba-Ahmed ya roki Tinubu da ya yi watsi da duk wani shirin sake tsayawa takara a 2027.

Baba-Ahmed ya bayar da hujjar cewa, Tinubu ya ajiye son ransa, ya bar matasa a mulki, ya fice daga Siyasa a mutunce, shi ne dattaku da barin baya da kyau.

Karanta Wannan  CIKIN HOTUNA: Rarara Ya Tallafawa Wasu daga cikin kin manoman Jihar Katsina, da Naira Miliyan Ashirin ( 20,000,000 ) Domin Suyi Chefanen Babbar Sallah

“Ka koma gefe – ba wai kabar wa abokan hamayyarka takara ba, amma don sabbin jini matasa ‘yan Nijeriya da za su iya ciyar da al’umma gaba da sabbin kuzari da tunani.” in ji shi.

Ya kara da cewa, ya kamata shugaban kasa ya yi tunani a kan nagartattun abubuwan da yake son bari bayanshi da kuma yadda tarihi zai tuna da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *