Friday, December 5
Shadow

Shugaban APC na farko, Bisi Akande ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Buhari a Kaduna

Shugaban APC na farko, Bisi Akande ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Buhari a Kaduna

Shugaban jam’iyyar APC na farko kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande ya jagoranci tawagar ƴansiyasa zuwa ta’aziyyar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Shafin Z na BBC ya rawaito cewa tawogar ta kai ziyarar ce gidan marigayin a jihar Kaduna ranar Laraba, inda Akande ya kwatanta shi da shugaba na gari wanda tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba saboda kyayawan ayyuka da ya yi a ƙasar.

Matar marigayin ne Aisha Buhari da kuma ɗansa Yusuf Buhari ne suka tarbi tawagar ƴansiyasar.

Akande ya nuna kaɗuwarsa kan mutuwar tsohon shugaban ƙasar, inda ya ce lokaci na karshe da suka haɗu shi ne lokacin da ya kai masa ziyara a Daura.

Karanta Wannan  Tsohon Ministan Muhalli lokacin Buhari ya bar jam'iyyar APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *