Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja a Najeriya (NSEMA) ta ce kimanin mutum 30 ne ake fargabar sun mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta auku a wani wurin hakar ma’adinai.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Galkogo na ƙaramar hukumar Shiroro.
Hukumar ta ce an kuma samu nasarar ceto mutum shida da rai, sai dai sun samu munanan raunuka.
Mahakar dai ta rufta ne a jiya Litinin lokacin da suke tsaka da aiki haƙar ma’adanai.
Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Zubairu Ahmad: