Monday, December 16
Shadow

Idan gwamnoni suka rage cin hanci za su iya biyan fiye da N60,000 – NLC

Idan gwamnoni suka rage cin hanci za su iya biyan fiye da N60,000 – NLC

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta ce gwamnonin jihohin ƙasar za su iya biyan foye da naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, idan suka rage cin hanci da rashawa da kuɗin da suka kashewa wajen gudanar da mulki a jihohinsu.

Aranar Juma’a ne dai ƙungiyar gwmanonin ta fitar da wata sanarwar da a ciki take cewa gwamnonin jihohin ƙasar 36 ba za su iya biyan naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata ba.

To sai dai a cikin martanin da ta mayar ƙungiyar ta NLC, ta yi Allah wadai da sanarwar gwamnonin.

Karanta Wannan  DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin cire kowanne irin haraji akan magunguna da kayan asibiti da ake shigowa da su ƙasar nan

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NLC, Benson Upah,ya fitar ya ce idan gwamnaonin suka mayar da hankali babu abin da zai hana su biyan mafi ƙarancin albashin.

”Koda nawa ne mafi ƙarancin albashi ba ma naira 60,000 ba, in suka rage kuɗin da suke kashewa wajen gudanar da gwamnati, sannan suka rage cin hanci da rashawa to za su iya biya domin tabbatar da walwalar ma’aikata”, in ji sanarwar.

A ranar Juma’a ne bayan wata ganawa da wakilan gwamnati ƙungiyar ƙwadagon ta buƙaci gwamnatin tarayya ta biya naira 250,000 a matsayin maf ƙarancin albashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *