Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima.
DAGA: Abbas Yakubu Yaura
Wani jigo a jam’iyyar, NNPP, Buba Galadima ya ce ba zai taba yiwuwa ɗaukacin yankin Arewa su samu ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya a zaɓen 2027 ba.
A wata hira da jaridar Sun, tsohon sakataren rusasshiyar jam’iyyar CPC, ya bayyana cewa a tsarin dimokuradiyya irin na Najeriya, masu zaɓe na da ƴancin yin zaɓi daban-daban.
Da aka tambaye shi ko ƴan Arewa za su zaɓi Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, ko kuma takwaransa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, Galadima ya ce, “Ba ma cikin còci; Ba ma cikin másallaci. Me ya sa za mu yi magana da murya ɗaya?
“Dimokradiyya kenan.”Idan ka haɗa mutane uku tare, kowa ya sami hanyar tunani daban-daban kan yadda za a magance wata matsala.”
Shugaban na NNPP ya kuma yi zargin cewa an dannen ƙuri’un jam’iyyar a zaɓen 2023.
“NNPP tana aiki sosai domin bayan zaben, mun gano cewa an danne mana kuri’u. Sama da miliyan biyar na kuri’unmu aka danne,” inji shi.