Friday, December 5
Shadow

Matar Wannan mutumin ta ràsù a ambaliyar ruwan data faru a Mokwa jihar Naija, hakanan jaririnsa da ‘yan uwansa 7 duk sun ràsù da kayan jikinsa kawai ya tsira

Wannan mutumin me suna Adamu Yusuf ya rasa iyalansa guda 9, matarsa daya da jaririn dansa da ‘yan uwansa 6 a ambaliyar ruwan da ta faru a Mokwa dake jihar Naija.

Shi ya fitone daga Tiffin Maza daya daga cikin kauyukan da lamarin ya fi shafa.

Yace da suka ji ruwan, sun fito waje inda yake kowa ya rike hannun kowa yace amma da ruwan yayi karfi sai ya tarwatsasu, yace yana ji yana gani haka ruwan ya tafi da iyalinsa.

Yace shima Allah ne ya tseratar dashi saboda ya iya ruwa.

Yace kayan dake jikinsa ma taimako aka bashi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: 'Yan Uwan me yada badala a Tiktok, Yahya Amerika sun taru sun masa dukan kawo wuka saboda zubar musu da mutunci da yake inda yace ya tuba ba zai kara ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *