
Saudiyya ta tura sama da jami’an tsaro 40,000 don tabbatar da tsaro yayin aikin hajjin 2025.
Da yake jawabi a wani bikin gagarumin faretin soji da aka gudanar a birnin Makkah, Mohammad bin Abdullah Al-Bassami, darektan tsaron jama’a kuma shugaban kwamitin tsaron hajji, ya ce dukkan sassan tsaro an tura su domin aiwatar da shirin tsaro na bana, tare da karin bayani cewa jami’an tsaron suna cikin shirin ko-ta-kwana kuma a shirye suke su dauki matakin gaggawa idan ya taso.
“An tanadi dukkan abinda ake bukata domin tabbatar da tsaron lafiyar mahajjata da jin dadinsu a lokacin aikin hajji,” in ji shi.
“Jami’an tsaronmu suna cikin matakin shiri mafi girma don fuskantar kowanne hali da zai iya barazana ga tsarkin wannan ibada.
“Muna da kwarin guiwar tabbatar da cewa mahajjata za su gudanar da ibadunsu cikin sauki da kwanciyar hankali.
“A bana, sama da jami’an tsaro 40,000 za a tura su zuwa manyan wuraren ibada kamar Makkah, Mina, Arafat da Muzdalifah.
“Tsarin tsaron ya kuma kunshi kara sanya ido ta hanyar na’urorin leƙen asiri, shirin gaggawa da kuma dabarun sarrafa zirga-zirga domin baiwa fiye da miliyan ɗaya na mahajjata damar motsi cikin tsari.”